KA ZAƁA MA ƳA'ƳANKA UWA TAGARI.
"Wasu mazan babu ruwansu da duba tarbiyyar macen da suke son su aura, su dai abin dubinsu kaɗai shi ne kyawun fuskarta, wanda shi kuma wannan kyawun yana tasiri ne a jikinta na wasu ƴan shekaru marasa yawa a rayuwarta"
-
"Duk yadda mace takai ga kyawu, to tabbas akwai lokacin da za ka nemi wannan kyawun a gareta ka rasa shi, amma shi kyawun halinta yakan yi tasiri a tattare da ita matuƙar ba shaiɗan ya canza mata ɗabi'a ba"
-
"Kada ka biye ma kyawun fuskarta, kada ka biye ma kyawun dirinta, ka nemi kyawun halinta da nagartarta, domin zaɓa ma kanka mace tagari mai kyawawan ɗabi'u, tamkar taimakawa ƴa'ƴanka ne wajen nema musu uwa tagari wacce za suyi alfahari da ita a duniyarsu da kuma lahirarsu, biye ma son zuciyarka wajen zaɓar mace mara kyawun hali kuma tamkar tozarta alfaharin ƴa'ƴanka ne"
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Facebook group
https://www.facebook.com/groups/4329860357034439/?ref=share