KARATU A BAYAN LIMAN
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum.
Wanda ke bin liman a sallar Azahar ne bai karanta Fatiha ba, shi ne yake tambaya a kan matsayin sallarsa. Ta yi, ko ba ta yi ba?
:
*AMSA*👇
:
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Sahihiyar magana a wurin malamai a kan mas’alar karatu a bayan liman ita ce:
Duk lokacin da mai sallah a bayan liman yake jin karatun limaminsa wajibi ne ya yi shiru ya saurare shi, saboda maganar Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala cewa:
وَإِذَا قُرِئَ ٱلۡقُرۡءَانُ فَٱسۡتَمِعُوا۟ لَهُۥ وَأَنصِتُوا۟ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Kuma idan ana karanta Alqur’ani sai ku yi saurare gare shi kuma ku yi shiru, domin ko a yi muku Rahama. (Surah Al-A’raaf: 204)
Sannan kuma a cikin hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« إِنَّمَا جُعِلَ الإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ »…. « وَإِذَا قَرَأَ فَأَنْصِتُوا »
An sanya liman ne domin a yi koyi da shi kawai… kuma idan ya yi karatu sai ku yi shiru. (Sahih Abi-Daawud: 617).
Sai kuma hadisin Jaabir (Radiyal Laahu Anhu), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
« مَنْ كَانَ لَهُ إِمَامٌ فَقِرَاءَةُ الإِمَامِ لَهُ قِرَاءَةٌ »
Wanda yake da limami, to karatun limaminsa shi ne karatu a gare shi.
Watau a inda limamin ya bayyana karatun.
Kodayake wannan hadisin yana da rauni idan aka yi masa duban farko, amma dai malamai masana hadisi sun amince da kafa hujja da shi, saboda albarkacin yawan hanyoyin da suka zo ta cikinsu. (Aslu Sifatis Salaah: 1/349-359).
Idan kuwa ba ya jin karatun limaminsa ko dai saboda a ɓoye yake karatun, kamar a Azahar ko La’asar, ko kuma saboda ya yi nesa daga inda ya ke, to a nan ya wajaba gare shi ya karanta shi ma, saboda maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:
« لاَ صَلاَةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ الْكِتَابِ فَصَاعِدًا »
Babu sallah ga duk wanda bai karanta Fatiha da abin da ya ƙaru a cikinta ba. (Sahih Abi-Daawud: 780)
Kafa hujja da wannan hadisin a kan wajibcin karatun mamu ko da kuwa yana jin karatun limaminsa ba daidai ba ne. Saboda dalilan da ya ambata a cikin Aslu Sifatis Salaah, Fasl a kan: Naskhul Qiraa’ah Waraa’al Imaam Fil Jahriyyah, shafi: 327-364).
Kuma idan da karatun wajibi ne a kansa meyasa a lokacin da ya zo ya samu liman a cikin ruku’u ba a ce ya tsaya sai ya karanta ta ba? Kuma meyasa a ƙarshe ba a ce ya rasa wannan raka’ar ba?!
Sannan kuma idan bai yi karatu a lokacin da ba ya jin karatun limaminsa ba, babu abin da zai yi sai dai tunane-tunanen al’amuran duniya kawai.
A taƙaice dai, abin da ya wajaba ga wannan mai sallah shi ne ya yi karatu a bayan limainsa a sallar Azahar da La’asar da raka’o’in ƙarshe na maghriba da Isha’i. Amma dayake bai yi ba - wataƙila - saboda rashin sani, to babu komai tun da yake a bayan liman ya ke. Sai ya kulawa saboda gaba.
Allaah ya ƙara mana fahimta.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ