KUSKURENA YA YIN DA NAKE
ALWALA
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*FUTOWA TA 👇*
*(13)*
*YIN TSARKI DA KASHIN DABBOBI KO QASHI*
Manzan Allah saw ya hana mutum ya yi tsarki da kashin dabbobi ko qashi kamar yadda yazo acikin hadisin Abdurrahaman bn zaid yace akace da salman shin Annabinku ya koyar da ku komai har shiga ban daki sai salman yace eh har shiga bayan gida sai dai ya hanamu mu fuskanci alqibla lokacin da muke fitsari ko bayan gida ko kuma muyi tsarki da dama ko kuma muyi tsarkin dutse da qasa da duwatsu uku ko muyi tsarki da kashin dabbobi ko qashi. Imamun nawawi yana cewa acikin wannan hadisin akwai hani dan gane da yin tsarki da najasa domin kashin dabbobi najasa ne amma shi kuma qashi abuncin aljanu ne qarqashin haka duk wani abun da ake ci ya shiga ciki kuma zaka shigar da ababe masu daraja ciki kamar takaddun da aka rubuta ilimi ko makamancinsa babu bam bamci tsakanin najasa daskararriya da mai ruwa idan mutum ya yi tsarki da najasa wajibine ya yi tsarki da ruwa domin a wannan lokacin dutse bazai wadatar dashi ba domin wajan ya zama najasa bayan najasa da take wajan.
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*MU HADU A FUTOWA TA 14*
*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏