KUSKURENA YAYIN DA NAKE SALLAH 10



KUSKURENA YA YIN DA NAKE
               SALLAH

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*FUTUWA TA 👇*
           *(10)*

*SHELAR MUTUWA ACIKIN MASALLACI*

   Idan muka koma tarihi zamu ga cewa shelar mutuwa aikine daga cikin aiyukan jahiliyya, musulunci ya hana aikata hakan, abun da ake nufi da hana shelar mutuwa shine ayi kira cikin mutane cewa wane ya mutu domin ayi gangami wajan jana'izarsa, amma gayawa iyalan mamaci da makusancensa cewa ya mutu domin su halarci wanke sa da shiryasa, wannan babu komai akan haka, saboda larabawa sun kasance idan mutum ya mutu sai su tura "yan aike a kofar gidaje da kasuwanni domin shelar mutuwarsa sai musulunci yazo ya hana aikata hakan, ya takaitasa akan iya makusantan mamaci, akan haka malamai suka kasa shelar mutuwa zuwa gida uku :

1- Sanar da "yan uwan mamaci da abokansa da mutane na kwarai suka ce wannan sunnah ne.

2- Sanar da jama'a masu yawa domin nuna Alfahri wannan an karhanta sa

3- Sanar da mutuwarsa da wani nau'in na daban kamar ihu da dukan jiki ko yaga tufafi wannan suka ce haramunne. 
   Babu shakka shela acikin masallaci zata shiga nau'i na biyu wanda Malamai suka kyamaci aikata hakan saboda akwai nuna Alfahri na tara mutane da yawa, saboda magabata na kwarai basu aikata hakan ba, akan haka SAN'ANI yake fada cikin littafinsa SUBULUSSALAM sharhin da ya yiwa BULUGUL MARAM yace zai shiga cikin shelar mutuwa sanarwar da ake yi akan manbura da kuma gidajen redio ya yin da wani babba ya mutu.

*ALLAH SHINE MASANI*

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

*MU HADU A FUTOWA TA (11)*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
          *(Abu Rumaisa)*
        🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)