MA’ANAR MUTU’A: AUREN WUCIN GADI
Mutu’a, ko kuma auren wucin gadi, watau auren da ba na dun-dun- dun ba, ma’anarsa shi ne namiji ya ƙulla jinga da mace cewa zai sadu da ita sau ɗaya ko sau biyu, ko kuma na tsawon awa ɗaya, ko kwana kaza, ko wata kaza, a kan kuɗi kaza ko ladan abu kaza.
Auren Mutu’a yana cikin aurace-auracen Jahiliya kuma an yi aiki da shi a farkon Musulunci kana daga bisani aka haramta shi. An karɓo ruwaya daga Ali binu Abi Ɗalib (R.A), cewa “Manzon Allah (SAW) ya hana auren Mutu’a da cin naman jakin gida a lokacin (yaƙin) Khaibar.” *[Bukhari da Muslim].*
Amma ƴan Shi’a sun ci gaba da halasta Mutu’a kuma sun ƙago ruwayoyin ƙarya waɗanda suka nuna falalarta da ɗumbin ladan wanda ya yi ta, da kuma darajarsa a aljanna. Babu shakka sun yi haka domin su ɓata al’ummar Musulmi ta hanyar yaɗa lalata da ɓarna da alfasha a tsakaninsu kuma don su jawo hankalin jahilai, musamman matasa, zuwa ga tafarkinsu.
*Falalar Mutu’a:*
Akwai ɗaruruwan ruwayoyi a cikin littafan malaman Shi’a da suke izna da su waɗanda suke nuna falalar auren wucin gadi. Ya zo a cikin littafin *Man La Yahduruhul Faƙih*, ɗaya daga cikin littafansu guda huɗu mafiya inganci, sun laƙa ma Ja’afar Sadiƙ, Imaminsu na shida, cewa ya ce: “Lallai Mutu’a addinina ce kuma addinin iyayena. Wanda ya yi aiki da ita ya yi aiki da addininmu kuma wanda ya yi inkarin ta ya yi inkarin addininmu, kuma ya yi riƙo da wanin addininmu.” [ *Ibnu Babawaih Alkummi, Man La Yahduruhul Fakih, bugun Darut Ta’aruf, Bairut, 1401 B.H., mujalladi na 3 shafi na 336].*
Ya zo a wannan littafi har yau, sun dangana ga Annabi (SAW) cewa wai ya ce: “Wanda ya yi Mutu’a sau ɗaya zai amince fushin Allah, wanda ya yi Mutu’a sau biyu za’a tashe shi tare da zaɓaɓɓun bayi, wanda ya yi Mutu’a sau uku zai haɗa kafaɗa da ni a aljanna.” *[A duba Man La Yahduruhul Fakih na Alkummi, muj. na 3 sha. 336]* . A wata ruwayar mai kama da wannan, sun ƙaga wa Manzon Allah (SAW) cewa wai ya ce: “Wanda ya yi Mutu’a sau ɗaya za ta zama (gare shi) kamar darajar Hussaini (A.S); wanda ya yi Mutu’a sau biyu darajarsa kamar darajar Hassan (A.S) ce; wanda ya yi Mutu’a sau uku darajarsa za ta kasance kamar darajar Ali (A.S); kuma wanda ya yi Mutu’a sau huɗu darajarsa kamar darajata ce.” *[Fatahallah Kashani, Tafsiru Minhajis Sadikin, bugun Maktabatus Sadar, Tehran-Iran, 1379 B.H., muj. na 2 sha. na 493]* .
Da yake mata suna da ƙarin kunya a kan maza, wataƙila za su buƙaci a ƙara ɗan ingiza su kaɗan kafin su faɗa ramin alfasha. Don haka Alƙummi, wanda suke yi wa laƙabi da Alsaduƙ (watau mai yawan gaskiya!) ya kitsa musu tasu ruwaya ta musamman. Ya ce, “Lokacin da aka yi isra’i da Annabi (SAW) zuwa sama, ya ce: Jibrilu ya riske ni ya ce: Ya Muhammad, Allah mai girma da ɗaukaka yana cewa: Lallai ni na gafartawa masu yin Mutu’a daga matayen al’ummarka.” *[A duba Man La Yahduruhul Fakih, muj. na 3 shafi na 463].*
*Ladan Mai Yin Mutu’a:*
Abinda ya gabata dangane da falala da ɗaukakar darajar mai yin auren Mutu’a ne. Amma dangane da ɗumbin ladan da zai samu, bari mu saurari Alsaduƙ ya ƙara shara mana ita. Ya ce: an tambayi Abu Abdullahi, watau Imamin Shi’a na shida: Shin mai yin Mutu’a yana da lada? Sai ya ce, “In yana nufin yardar Allah da ita (Mutu’ar) ba zai yi magana da ita ba (matar) kalma guda face Allah ya rubuta masa lada da ita (kalmar), kuma idan ya kusance ta sai Allah ya gafartar masa zunubi, kuma idan ya yi wanka Allah zai gafarta masa da gwargwadon ruwan da ya shuɗe a kan gashinsa.” *[Man La Yahduruhul Fakih, muj. na 3 sha. na 336].*
*Gargaɗi ga Wanda Ya Ƙi Yin Mutu’a*
Bayan bayanin falala da garaɓasar Mutu’a, idan da akwai wani mai taurin kai wanda ya ƙi ɗibar wannan garaɓasa, to sai a yi masa gargaɗi kuma a tsoratar da shi. Wannan shi ne abinda malamin Shi’a, mai suna Alfailul Kashani, ya yi a yayin da ya ruwaito daga Annabi (SAW) cewa wai ya ce: “Wanda ya fita daga duniya bai yi Mutu’a ba, zai zo ranar Alƙiyama yana yankakke (watau naƙisin halitta).” [ *A duba Minhajus Sadikin na Kashani, mujalladi. na 2 shafi. na 489].*
A harshen Shari’a, irin wannan gargaɗi ana yin sa ne ga wanda ya aikata kaba’ira, watau babban zunubi, kamar shaidar zur, ko gudu daga fagen fama, ko saɓa wa iyaye da sauransu.
Saboda haka za mu fahimta a nan cewa, ƙin yin Mutu’a dai-dai yake da aikata kaba’ira. Kuma wannan babu mamaki idan muka dubi waccan ruwaya da ta gabata wacce take cewa, “Wanda ya yi inkarinta ya yi inkarin addininmu.”
Wannan ya sa Sayyid Hussain Almusawi, wanda a da ɗan Shi’a ne kuma Allah ya shirye shi ya tuba, yake cewa manyan malaman Shi’a na wannan zamani, kamar su Sayyid Assadar da Alburujardi da Asshirazi da Alƙazwini da Alɗibaɗiba’i da Abu Harith Alyasiri da kuma uban tafiya, Imam Khumaini, duka suna yin Mutu’a, kuma suna yin ta da yawa ba kaɗan ba! [ *Sayyid Hussain Musawi, Kashful Asrari wa Tabri’atil A’immatil Adhari, bugun Darul Iman, Alkahira, 2002, sha. na 34-35].*
A bisa mafi rinjayen zato, Rafilawan Nijeriya ma suna yin mutu’a, kuma Mutu’a na cikin hanyoyin yaudara da suke jawo hankalin jahilai da su, musamman matasa maza da mata, zuwa ga wannan tafarki nasu mai nufin rushe durakun al’umma.
*- JERIN LITTAFAN SHI’A NA 4: "Auren Mutu’a a wajen Ƴan Shi’a" - na Prof. Umar Labɗo*
*✍ AnnasihaTv*
```- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka``` ;
*Call/WhatsApp:* 08142286718
*Twitter*: https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09