GUZURIN MA'AURATA DAGA HADISIN ANNABI S.A.W



*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*
 
_*Daga zauren*_
_*📚Ana- muslim📚*_
*_💝 GUZIRIN MA'AURATA DAGA HADISAN ANNABI. (ﷺ) 💝_*
*_{{ Darasi na //66}}_*
°
_✍🏽 An karɓo daga Abi Sa’eed Alkhudry (RA) cewa: Tabbas mãta sunce: “Yã Manzon Allah (SAW) ! Maza sunyi rinjãye a gunka; don haka ka saka mana wata rãna da za mu dinga zuwa kanã yi mana wa’azi”..._

_✍🏽...Sai Annabi (SAW) yayi musu alƙawarin, sai yayi musu umurni da abin da ya wajabta a kansu yayi musu wa’azi kuma yace: (( Cikinku bãbu wacce ƴãƴanta ƙanãna guda uku za su mutu; face, sai sun zamo mata kãriya daga Wuta ))..._

_✍🏽...Sai wata mace tace: “ko da biyu ne?” Sabõda ni ƴãƴãna biyu sun mutu, sai Annabi (SAW) yace: (( ko da biyun ne ))._
*Bukhary.*

_✍🏽 Wato wannan Hadisi na nuna mana abubuwa kamar haka: yiwa mãta wa’azi ko karantar da su abu ne da yake da asali a Addini, sai kuma wanda ƴãƴansa/ta biyu zuwa uku suka rasu kãfin balaga suka yi haƙuri bisa hakan, sai mutum yayi haƙuri ya mayar da lamarinsa ga Allah, ba tãre da ƙõrafi ba._

_✍🏽 Tausayin Annabi (SAW) ga al’umarsa, ƴãƴan mutum za su zamo masa/ta hijabi/kãriya daga wuta, za a ce da ƴãƴan: ku shiga Aljanna ! sai su ce: ba za su shiga ba; sai tãre da Iyãyensu. Allahu Akbar._

_✍🏽 Amma fa hakan sai ƴãƴa ƙanãnu waɗanda basu balaga ba, akwai ma wata riwayar da ta ce har ma waɗanda suka rasa ɗã/ƴã ɗaya._
.
```Allah ya kyautta ƙarshen mu```
*_🖋 Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}_*
_​​Gabaτarωa : *Sadeeq Nagogo{βlυηğυ}​​*_
.
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
~~
_DAGA: *ZAUREN ANA MUSLIM*_
_*08093347777*_
_*08085777555*_
~~~
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ ɴα ғαcєвooк ѕαι α lαtsα ɴαɴ​​ ⬇*_
https://www.facebook.com/Ana-Muslim-Group-156263338266984/
Post a Comment (0)