MAKARANTAR ISLAMIYYA //01
SHUGABANCIN MAKARANTA.
Dukkan masu karantarwa a makarantun Ibtida'iyoyinmu kan koka da matsalolin shugabanci a makarantun da suke karantarwa sai É—an waÉ—anda ba a rasa ba. Matsalolin kuma galibi su kan samo asali ne daga;
A- Rashin iya gudanar da aikin shugabancin.
B- Sanya mugunta da son zuciya wurin gudanar da shugabancin.
C- Rashin samun cikakken ikon gudanarwa a lokacin da makaranta ke ƙarƙashin wani kwamita ko makamantansu.
RASHIN IYA GUDANAR DA SHUGABANCI.
Wasu shuwagabannin makarantar ba su iya aikinsu ba ne, ko dai saboda rashin cancanta ko kuma saboda rashin ilimin yadda ake gudanarwan, ga irin waÉ—annan dole a canza wanda bai cancanta ba, a ilimantar da wanda bai san tsarin gudanarwa ba. Shi dai shugaban makaranta (Headmaster) aikinshi shine ya "tsara kuma ya kyautata yadda za a yi amfani da mutane da kuma sauran kayan amfani domin a cimma wata tsararriyar manufa ta makaranta" wannan zai nuna mana lallai dukkan shugaba dole ne ya samar da :
1- Tsari da manufar da makaranta ke buƙata ta cimmawa a rubuce.
2- Tsarin amfani da mutanen da za su yi aiki tare don cimma waÉ—annan manufofi.
3- Tsarin amfani da sauran kayayyakin aikin da ake buƙata domin cimma manufofin da aka tsara.
In shugaba bai iya samar da waÉ—annan tsare-tsare ba, to ko dai a ilimantar da shi ya gyara ko kuma in ba zai iya ba a canza shi.
SANYA MUGUNTA KO SON ZUCIYA A GUDANAR DA SHUGABANCI.
A nan kuma shugaba ya cancanta kuma yana da ilimin tsarin amma sai a samu ya sa son zuciya ko mugunta wurin aiwatar da tsarin, kamar ƙin yin abinda ya san aikinshi ne, ko ƙin bayar da wani haƙƙi ga wanda ya cancance shi, ko tattare ayyuka ga kanshi shi kaɗai alhalin kuma ba zai iya gudanar da su baki ɗaya ba, misali ka ga shugaban makaranta shine : Me karɓar kuɗin makaranta, shine shugaban jarabawa, shine karɓar kuɗin sauka, shine mai saida form ɗin ɗaukar ɗalibai, shine mai tsara yadda za a yi sauka da duk wani aiki da ya kamata a ce ya rarrabasu ga abokan aikinshi, ko kuma a samu wani shugaban 'yan uwansa da makusantansa ne kawai aka tara a makarantar ba tare da duba cancantarsu ko rashinta ba.
In aka samu irin haka lallai wajibi ne in akwai na sama da waÉ—annan shugaba su shigo ciki su gyara tsarin zuwa ga abinda yake shine ya dace, daga cikin hanyoyin gyaran irin wannan matsala in akwai na sama da shugaban a samu :
1- Sa ido (supervision) kan yadda komai ke tafiya.
2- A riƙa duba cancanta ba kusanci ba wurin bada wani aiki ga wani don ci gaban makaranta.
3- A riƙa samun rabon ayyuka, ba a tattare ayyuka a wuri ɗaya ba.
4- A riƙa sa tsoron Allah a dukkan komai.
In babu na sama da shugaban kuma, to lallai a samu waÉ—anda za su bashi shawari cikin malaman makarantar cikin tausasawa da hikima har ya fahimci ina aka sa gaba.
RASHIN SAMUN IKON GUDANARWA SABODA MAKARANTA NA ƘARƘASHIN KWAMITI KO MAKANTANSHI.
Irin wannan yanayi na da matuƙar wahalar sha'ani sosai, domin shugaba kan rasa mafita a wani lokaci, ƙarshe wani lokaci in shugaban mai son aiki ne da samar da cigaba sai dai ya haƙura ya aje aikin, ko kuma ya haƙura ya bi tsarinsu ya dace ko bai dace ba. To idan irin haka ta faru ana iya bin hanyoyi kamar haka domin a samu dacewa :
1- Tattaunawa ta lumana da fahimtar juna.
2- Shigo da wasu masana cikin abin domin su ji shawararwarin daga wasu bakunan.
3- Tattaunawa da É—aiÉ—aikunsu domin fahimtar da su manufofinka da tsarinka.
4- Yin amfani da kuɗinka wani lokacin don gudanar da wasu ababen da ke buƙatar kashe kuɗi.
5- Haƙuri, da karɓar shawara a lokacin da wasu suka saɓa maka kuma basu fahimce ka ba.
Daga ƙarshe ya kamata dukkan wani shugaban makaranta ya tabbatar yana da cikakken tsarin sanin abubuwa kamar haka :
1- Manufar makarantar da yake shugabanci kan É—aliban (me ake so É—alibi ya samu na ilimi kafin a yaye shi).
2- Tabbatar da yawan É—aliban kowanne aji tare da taskance bayanan kowanne É—alibi (cikin file É—insa) da kuma bayanan zuwa da rashin zuwansa cikin rajista.
3- Tantance bayanan biya ko rashin biyan kuÉ—in makaranta daga É—alibai.
4- Tabbatar da biya ko rashin biyan malamai.
5- Tabbatar da zuwa ko rashin zuwan malamai da kuma tabbatar da suna aikinsu yadda makaranta ke buƙata.
6- Tabbatar da É—alibai na samun ingantattun tarbiya da ilimi.
7- Tabbatar da samuwar dukkan abin da malamai da ɗalibai ke buƙata don karatunsu.
8- Tabbatar da bin dokoki daga malamai da É—alibai.
In muka lura za mu ga ayyukan na da yawa da wuya shugaba ya iya gudanar da su shi kaɗai, dole sai da taimakon wasu to anan ne maganar raba muƙamai za ta taso wacce za ta zama itace matashiyarmu ta gaba.