MANUFATA

Manufata.....




 Bana bukatar turbar lusari.
Allah ya tsaremu da sharri.
A hanyar Sakkwato Faskari.
A Jigawa akwai Maigatari.
Mai mulki shi ne mai gari.
Gaskiya ce gata a zahiri.
Marubuta sun wuce tsaburi.
Haskensu tamkar taurari.
Tsokana ke kawo tunzuri.
A cikin girki za ka ga turiri.
So nake ni ma na yi kokari.
Burina na zauna da sha'iri.
Masu son kullum nai hanzari.
Zuciyata daina yawan bari.
Shi ilimi tushe ne mafari.
Idan jahilci ya yi ma k'ari.
Daka wuce sai tashin k'auri.
Ga goro na nan bari-bari.
Yanzu ne zan ware gwari.
Babu abinda yake mini kari.
Don k'asan gwiwane kwauri.
A itace har da ma dakasari.
Karamin yatsane d'ankuri.
Sanadi shi ne fa mafari.
'Yan kad'an su ne fa tsirari.
Mai hadama shi ne mai zari.
Na ga daurarre a cikin mari.
Fitinanne shi ne matsari.
Matsiyaci ga shi da Fakiri.
Hanyar banza tai sunturi.
Fanke shi ne mai kumburi.
Shi abin cizo kuma hakori.
Barazana ita ce kuma kurari.
Mai fankama shi ne mai kuri.
Mai bada tarbiyya ko mahori.
Magulmaci shiyake yin tsiri.
Mai d'inki yana son mazari.
Mai suya zai nemi kwangiri.
Basarake ga shi da kwagiri.
Shi abin so ne kuma hakuri.
A cikin abokai akwai nagari.
Masu bayarwa shawarwari.
Shi ko mai taurin kai ja'iri.
A idon wasu ga shi kwazari.


(C)Aliyu Idris Jigawa
24/11/2022
Post a Comment (0)