SHI ZAN IYA YIWA YARONA BAYANI AKAN ZINA? (WANDA BAI BALAGA BA)

SHI ZAN IYA YIWA YARONA BAYANI AKAN ZINA? (WANDA BAI BALAGA BA)


https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu'alaikum mlm wata tambaya yarona yayimin dazu 
 Yana gayamin irin karatun da akaimusu amakarantane da irin wa'azin da akaimusu,abinda Allah yahana da wanda yace ayi,to Wanda baiganeba saiyatanbayeni inmasa karin bayani,to anacikin haka sai akazo kan aikata ZINA shine yatanbayeni wai mene ZINA
Nikuma nacemasa sai yakara girma zanmasa bayani kokuma inyagirman yasani dakansa inlokacin sanin yayi, daya takuramin sainacemasa sainatanbaya in'ance ingayamasa sai ingaymasa.

   Wallahi mlm budan bakin yaron sai yacemin yasan innatanbaya din cemin za'ai ingayamsa sabida inyagirma yakiyaye.
   To yanzu mlm yakai girman dazan masa bayani akan ZINA kuwa? Skeharar 8 darabi?
:
*AMSA*👇
:
Bai kai Girman da Zaki Gaya Masa Me Ake Nufi Da Zina ba. Kar ki gaya masa. Ki gaya masa wani Abu a Matsayin Cewar Wannan Abin Shi Ake Nufi da Zina. Sabida Wani Lokacin Rashin Sanin Abu ga Yaro Shine Alkairi a gare shi da shi da iyayensa. 
  Misali. Zaki Iya ice Masa, Abinda Ake Nufi da Zina Shine, Shiga gidan Mutane ba tare da kayi SALLAMA ba. Insha Allahu zai Kiyaye. Amma ayi Masa Bayani Akan Zina Bai Kai ba gaskiya. Idan Aka yi Masa wannan Bayanin. Duk Lokacin da Yaga wani Namiji Shi da Matar da Matarsa ba. Kai da matarsa ta Aure sun kebanta ko sun fito daga wani gida. Zai dauka Zina Suka yi. Haka idan Yaga wani ya shiga wani gida zaice Zina yaje yayi da Matar wannan Gidan. Sabida yaro ne. Bai kai ya Tantance yadda komi yake ba.
  Wajibi ne Malaman Islamiyoyi Suna Kallon Hankali da Shekaru Na Yaro. Sai su bashi ilimi Daidai da Tunaninsa da kuma Hankalinsa.
  Yaron da bai Wuce Shekaru 8 ba. Bai Wuce a bashi Ilimi Akan Tsarki da Sallah da Alwala da Sanin Allah da Manzon sa ba. da soyayya ga Allah da Manzon sa da Son Iyalan Gidan Manzon Allah Saw da son Alqur'ani da Nunawa yara Biyayya ga Iyaye da girmama Manya da Tausayi Kananan yara na kasa da su da tsafta. Sannan su Iya Alwala da sallah da Ziyarar yan Uwa da Sauransu.
  A fagen Sira Kuwa, Ma'ana Tarihi Shine. Koya Musu tarihin Magabata na Kwarai (Sahabbai da Tabi'ai) Da yadda Suka yi Gwagwarmayarsu wajen yada Addinin Allah da Hakuri da Jarumta da yadda Suka ci gaba da biyayya ga Allah da yadda Suka Cigaba da yada Addinin Allah bayan Rasuwar Manzon Allah saw har suka bar duniya.
  A shawarar da zan Baiwa Malaman Islamiyya, su da Malamansu. Wajibi ne Ana Shiryawa wadannan Malaman Islamiyyar Wata BITA (Seminar) da za'a ke koya musu Asalin Abinda ma zasu koyar ga dan Aji Daya haka dan Aji biyu, har zuwa Aji Shida. Ma'ana daga Wannan Matakin Zuwa Wancan Matakin. (From Simple to Complex). 
 Sannan Kuma Wajibi ne Za'a koyawa Wadannan Malaman Islamiyyar Yadda Zasu Mu'amalanci Wadannan Daliban da Suke Koyarwa. Sabida wani Lokacin zaka Samu a Wasu Islamiyoyin, Su Kansu Malaman Makarantar, Samari ne masu Matsakaicin Shekaru, Masu Tashen Balaga. Haka Daliban Ma Zaka samu Yan Mata ne, ko kuma da yan Mata a Cikinsu, Masu Tashen Balaga. Sai ka Samu Wadannan Malaman Babu Ko Guda daya da yake da Aure. 
 Sabida Haka. Wajibi ne Sai an koya Musu Yadda Zasu Zama Masu Kamun Kai. Kar suna Wasa da wadannan yan matan. Sabida Shaidanin da yake Tsakanin su, Yafi Shaidanin da yake Gidan Giya ko Gidan Karuwai Hadari. Sai ya ga yadda zai Kautar sa Mutanen Kirki daga Turba Mai Kyau. Ko ya kawo Wata Fitina a wajen Addini.
  Sannan Wajibi ne a Koya Musu yadda Ake Punishment, Ma'ana Horar da Dalibi ko Daliba a Makaranta, idan Yayi Lefin da Za'a bashi Horo. Domin ana samu, zaka ga Wani Malamin, Yana da Tsananin Zafin Rai. Sabida haka Kenan Kaga Irin Wadannan Masu Zafin Ran. idan ya kama Dalibi ko daliba da Duka. Wani zaka ga bayan Amfani da Bulala ma har da Sa Hannu da Kafa da Sauransu. Ko ya dauki Wani Karfe ko Wani Makami ya Dokawa dalibi ko daliba akan Lefin da bai kai ya kawo ba.
Wannan ya taba Faruwa. Wani Malamin Islamiyya, da ya sami wani dalibi ya doke Shi a Ido, sai da Idon yaron ya Rufe ya dena gani. Inaga sai daga baya ne Aka Samu yaron ya Warke. Menene Amfanin Irin Wannan.? Kaga Kenan, Wajibi ne Sai ana Saita wadannan Malaman Islamiyyar Akan Yadda Zasu ke Yin Punishment. Wani Lokacinma Tsawa da zaka Yiwa Dalibi Ko Daliba ya Isa.
  Haka zalika. Wani fa wani Malamin Zai bar Abinda ya kawo shi na koyar da dalibai. Sai ya Buge da soyayya da Dalibai. Sai ka ji ance wance ta Aji Hudu budurwarsa ce, wance ma ta Aji biyar budurwarsa ce, wance ma ta Aji Shida Budurwar sa ce. Ma'ana duk idan ya Kyalla ya ga Daliba Mai kyau ko mai Haske, Shikenan magana ta Kare. Sai ya Kulla Alaka ta Soyayya da Ita. Wanda a Haka Fa. Har sai ya Wargaza Wannan Makarantar, ba'a Amfana da Ilimin da Allah ya bashi ba. Maimakon Malami ya zama Mai Kwarjini ga Dalibai. Wanda da Sun ganshi, zasu shiga Hayyacinsu. Sai dai kaga yana Dorin Alqur'ani ko yana dorin Hadisi A Daidai Lokacin Kuma Yana yiwa wata kallo irin na india da suke yiwa Masoyansu. Har sauran Dalibai su gane Shi. Shikenan daga wannan Ranar An Rena Malami Kenan.
 Haka zalika. Wajibi ne Malamin Islamiyya ya zama mai kyakykyawar Shiga a duk Lokacin da zai je Makaranta. Sabida Dabi'a Irin ta Mutum. A duk Lokacin da ya ganka Haka-haka. Ma'ana babu Tsafta a Tattare da Kai, babu Wasu Kaya Masu Kyau ko Tsada a tare da kai. Zai Rena Ka. Zai Dauka Cewar kai Wani Kaskantacce Ne. Alhalin Kuma gashi Allah ya Baka Alqur'ani. Manzon Allah saw Yace, Duk Wanda Allah ya bashi Alqur'ani yake ganin Akwai wani Mutum a Doron Duniyar Nan da ya Fi shi Falala. To ya Wulakanta Alqur'ani.
  Sabida haka kenan. Wajibi Ne Malamin Islamiyya ya zama mai Tsafta.
  Sannan a wajen bitar nan. Wajibi ne a Maida Hankali wajen Baiwa Wadannan Malaman Islamiyya din Ilimi Sosai. Sabida zasu dinga jin Tambayoyi daga wajen Daliban su. Kaga idan har Malami mai amsa sunan Malami babu Ilimi ae an Sami Matsala. Dalibi ko daliba Idan suna da Tambaya. Sai sun je Islamiyya suke Gabatar da Wadannan Tambayoyin Nasu. Domin Sunje Center Of Learning. Sabida haka kenan. Idan Malami ba Ilimi Kaga anan ma an sami Matsala. Duk da Cewar za'a Iya Bijirowa Malami kowa ye shi kuwa da Tambayar da bai sani ba. Amma dai ba zai yiwu ace Malam menene Hukuncin Abu kaza ka kasa yiwa dalibai Bayani. Sabida basu da Wanda ya Wuce kai Malamin su. Haka zalika kar Malami wai ya ji kunyar idan bai san Abu ba ya Jefa dalibansa cikin Kuskure. Wannan ma ba Daidai bane. Idan Baka sani ba kawai kace ban sani ba. Ko kace a Baka Lokaci zaka yi Bincike ko zakan Tambayi Malaminka. Domin Duk Malamin da Bashi da Malam An Sami Matsala.
  Haka zalika Iyayen Dalibai, Wajibi ne Kuna Girmama Malaman Islamiyyar da suka Dauke Muku Nauyin Karantar da Yayanku. Kuna Basu Hakkinsu na Koyar da Yayanku da Matan Ku da Suka Yi. Sannan Kuma yana da kyau Lokaci bayan Lokaci Kuna Yimusu Ihsani.
 Haka Zalika Kuma kuna Daukar Yayanku kyawawa kuna Aurawa Wadannan Malaman. Kar Sai An Ga Yarinya Mai Muni. Wadda ta Rasa Mijiin Aure. Sai Ace Ayiwa Malam Wane Tayi ko zai Aura. Wannan Bakwa Yiwa Malaman Islamiyya Adalci. Suma Fa Suna Son Kyakykyawar da kowa yake So.
 Bai Kamata Mutane Suna Daukar Malaman Islamiyya a Matsayin Kaskantattun Mutane a Cikin Al'umma ba. Indai Wadannan Malaman Sunnah Suke Koyawa Yayanku ba Bidi'ah ba.
 Kuma Wallahi Duk Wadda ta Auri Malamin Addini ta Chaba. Domin ba zata Rayu a Cikin Kuskure ba. Haka zalika duk Lokacin da tayi ba Daidai ba, Za'a yimata Uzuri. Ga Dumbin Ilimi da zata Samu. Sannan zata Iya Alqur'ani da Tajwidi.
 Magabata Suna Aurar da Yayansa ga Dalibansu. Amma a irin wannan Lokacin, idan yarinya ta kawo Malamin Islamiyyarsu Tace Shi take So. Nan da nan Iyayenta Za su taka Mata Birki. Sabida Suna ganin Wai zata Tona Musu Asiri. Me zai hana ba zata auri wani babban Ma'aikacin Gwamnati Mai karbar Salary ba ko kuma Wani babban dan Kasuwa ba. Ta yadda Zai Dauki Nauyin ta akan duk Abinda take so ba. Su ma kuma ya dauki Nauyin su ba?
Allah ya sawwake.
 Wai sai ka ga Malamin Islamiyya yana Koyar da yayan Mutane. Ba wanda zai Bashi Diyarsa, Sabida Abinda yake Yimusu na kyautatawa. Sai dai a bar shi Yana ji yana Gani. Sai dai ya Koma Kauyensu ya Auro wata Haka-haka.
 Allah ya Sawwake.
 Ku ma Malaman Islamiyya kuna yin Sana'a kuma kuna hadawa da Ilimin Zamani. Ku Zama yan Boko. Domin Boko Bata Yiwa Wanda ya Iya Alqur'ani Wahala. Ku samu kuna Hadawa da Aikin Gwamnati da Kasuwa. Ta haka ne zaku zama masu Kwarjini a Idon yan Matana Zaminn Nan da su da Iyayensu. Domin Duniya ga Gama Shiga Zukatan Mutane.
 Allah ya Kyauta.

Allah Shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797

GROUP ADMIN:👇
Mal. Khamis Yusuf
+2348087788208
+2348054836621

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)