TA YA MURNAR KIRSIMETI HARAMUN NE GA MUSULMI.

TA YA MURNAR KIRSIMETI HARAMUN NE GA MUSULMI.



Acikin Alƙur’ani Maigirma ALLAH (ﷻ) Ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَىٰ أَوْلِيَاءَ ۘ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ

Ma’ana: “Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi Yahudawa da Nasara masoya. Sashinsu masoya sashi ne. Duk kuwa cikin ku wanda ya jiɓinci lamarin su, toh lallai shi yana cikin su. Lallai ALLAH ba ya shiryar da mutane azzalumai.” [Maidah: 51]

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا عَدُوِّي وَعَدُوَّكُمْ أَوْلِيَاءَ تُلْقُونَ إِلَيْهِم بِالْمَوَدَّةِ وَقَدْ كَفَرُوا بِمَا جَاءَكُم مِّنَ الْحَقِّ

Ma’ana: “Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi maƙiyanku masoya, kuna nuna musu soyayya, alhali kuma sun kafircewa abunda yazo muku na gaskiya …” [Muntahana: 01]

Waɗannan ayoyin suna tabbatar mana da yadda ALLAH (ﷻ) Ya tabbatar mana da haƙiƙanin cewa lallai Yahudawa da Nasara ba masoyanmu bane face maƙiya ne agare mu, kuma yana nuna mana cewa wajibi musulmai su kasance masu tsayuwa da ƙafafuwansu, masu ji da girman su na kasancewar su musulmai; kada su kasance ƴan amshin shata ga maƙiyansu kafirai, su rinƙa yi musu biyayya sau da ƙafa a cikin shanin addininsu da ɗabi’unsu, wannan ƙasƙanci ne da tozarta kai.

Kuma ALLAH (ﷻ) Ya gargaɗe mu da bin son zuciyar yahudawa saboda akwai girman haɗari acikin yin biyayya ga manufofin su a rayuwar musulmai.

Ya kamata musulmai su sani cewa hukuncin ALLAH yafi ko wane hukunci inganci da adalci, don haka yayin da bawa ya fahimci haka, ya kamata ya ƙara miƙa wuya ga hukunce-hukuncen Ubangijinsa ko da kuwa bai gane hikimar da take cikinsu ba.

Babu Wani dalilin da zai sanya musulmi taya murnar wata idi na Yahudawa da Nasara bayan ALLAH (ﷻ) Ya bayyana mana su a matsayin maƙiyansa kuma maƙiya ga addininsa kuma waɗanda suka jingina masa abokan tarayya bayan ya tabbatar da cewa kada a haɗa shi da kowa.

Bukukuwar Kirsimeti, yana daga cikin abunda masu bautar kuros suka Keɓanta da shi, amma idan Musulmi ya yi tarayya da su acikinsa, toh kamar yana goya musu baya ne, kuma yana bayyana sonsa da addininsu, da ƙoƙarin shiga cikin rigarsu, da yarda da aƙidarsu.

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Duk wanda yake kama da waɗansu mutane, toh yana cikin su.” [Abu-Dawud ya ruwaito shi]

Kuma Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Mutum Yana tare da wanda yake so.” [Bukhari da Muslim suka ruwaito]

Wani irin kamanni ake nufi? Ba wai kamanni ta siffa (halitta) ba, kamanceceniya na addini da ɗabi’u, duk wanda ya kwaikwayi wata ɗabi’a ta Yahudu da Nasara toh yana tare da su, domin addinin musulunci yayi hani akan kamanceceniya da su, asali ma musulunci yana ƙira ne da a saɓa musu a dukkan aƙidunsu da ɗabi’unsu da addinin su baki ɗaya.

Yana daga cikin Adalci na addinin musulunci daga faɗin Manzon ALLAH (ﷺ) cewa zaka kasance tare da wanda kake so, wannan shi ma yana ƙara tabbatar mana duk musulmi da ya nuna soyayya da ƙauna ga kafirai toh zai kasance tare da su.

Umar Bn khaɗɗab (RA) yana cewa: “ku nisanci maƙiya ALLAH, YAHUDAWA da NASARAWA a ranar da suke haɗuwa suke gudanar da bukukuwansu, domin fushin ALLAH yana sauƙa akansu, ina jiye muku tsoron kada kuma ya shafe ku.” [Baihaqy ne ya fitar dashi cikin Sha’abul Imaan]

Sheikh Ibnu Bazz (Rahimahullah) Ya ce: “Ba ya halatta ga musulmi ko musulma su yi tarayya da yahudu da nasara ko wasunsu cikin bukukuwan Idinsu (ta hanyar taya su murna/ce musu happy christmas da sauransu), wajibi ne barin yin hakan domin duk wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane to yana cikinsu, Manzon ALLAH (ﷺ) kuwa ya gargaɗemu a kan kamanceceniya dasu da ɗabi’antuwa da ɗabi’unsu, saboda haka wajibi ne musulmi da musulma su kiyayi wannan kuma ba ya halatta su taimaka da komai a cikin wannan domin Idi ne da ya saɓa wa Shari’a.” [Majmu’ul Fatawa 6/40]

Sheikh Salih Al-uthaymeen (Rahimahullah) Ya ce: “Taya kafirai murnar Kirsimeti ko waninsa daga idinsu na addini haramun ne bisa ittifaƙi.” [Majmu’ul Fatawa 3/451]

Malaman musulunci sunyi ittafaƙi akan haramcin taya kafirai murnar Idin su, domin yin haka saɓawa umurnin ALLAH ne na kaɗaitakarsa, ta ya su murna kuwa jefa kai halaka ne domin yarda ne da dangantawa ALLAH abunda ya korewa kansa. Don haka wajibi ne musulmi ya kiyaye.

Ibnul Qayyim (Rahimahullah) Ya ce: “Taya arna murnar Kirsimeti haramun ne, Kuma babu Saɓani akan hakan, haka ma yin Azumi irin nasu, ko kaji yana cewa: “Idin ku yayi Albarka, Ko ina taya ku Murna, da makamantan haka, idan mai faɗar haka ba kafiri bane,Toh ya aikata haramun, saboda kamar yana taya su murnar yiwa Kuros sujjda ne, Kuma hakan shi ne mafi girman zunubi a Wajen ALLAH, Kuma mafi muni fiye da shan giya, da kashe rai, da zina da makamantan su, Kuma mafi yawan waɗanda basu da ruhi na addini, suna faɗawa cikin hakan, ba tare da sun san munin hakan ba, duk wanda ya taya wani bawa murnar yin zunubi ko bidi’a, Ko Kafirci,Toh zai iya jawowa kansa fushin ALLAH da Kamun sa.” [Kitaab Ahkaam Ahluz zimmah] 

Sau da yawa zamu iya cewa ilimi ya shiga lungu da saƙo na al’ummah, kuma malamai suna iya ƙoƙarinsu wajen ganin al’ummah sun kasance akan hanya madaidaiciya, su kuwa Al’ummah akwai da dama waɗanda saƙon gaskiya ta riske su amma saboda jahilci da son zuciya da kuma ɗaukan jahilci a matsayin wayewa hakan ya jefa su halaka ta yin koyi da maƙiya Yahudu da nasara da karrama al’adunsu da ɗabi’unsu. 

Al’amarin yin tarayya da kafirai a idodinsu da bukuwarsu yana da girman zunubi kuma mafi muni fiye da zunuban da aka haramta, domin babu abunda ya kai yiwa ALLAH shirka girman zunubi.

“Abinda mutane basu gane ba shi ne: a lokacin da kake yin murnar christmas (Kirsimeti) tamkar kana riya cewa lallai Annabi Isah (A.S) an haife shi ne a ranar (25) na watan December, sannan kuma kana riya cewa lallai shi Ɗa ne ga ALLAH, wanda kuma hakan yana bayiwa ne zuwa ga shirka, SubhanAllah.” Dr. Zakir Naik. (Hafidhahullah)

Yanzu ashe ka ƙira kanka musulmi amma kana taya murnar bikin haihuwar ɗan ALLAH? ashe kana musulmi kana farin cikin wata rana da ake yin idi saboda sanyawa ALLAH kishiya? Ya kai Musulmi Kaji Tsoron ALLAH ka zama nagartaccen musulmi mai imani a ciki da waje ba wai a fatar baki kawai ba.

Idan har kai musulmi ne an faɗa maka an sake faɗa maka kuma ana kan faɗa maka haramun ne Taya murnar Kirsimeti ta hanyar cewa: “Happy christmas da duk wata taya murnar da ya shafi haramci ga musulmi, domin ka sani cewa wannan kalma tana iya fitar da mutun daga musulunci. Domin da kace wa me kirsimeti happy Christmas gwara ka taya me laifin kisan kai, ko zina, ko luwaɗi, ko shan giya murna.

Malamai suka ce kalmace wacce take iya fitar da mutun daga musulunci kuma taj awo maka fushin ALLAH.

Wajibi ne duk musulmi ya sani cewa Musulunci idi biyu yake da shi ako wace shekara, Idin sallar azumi (idul fiɗr) da Idin sallar layya (idul Adha) sai kuma Idin da musulmai ke da shi a kowane sati/mako wato ranar Juma’a.

Duk wani idi da yake saɓanin waɗannan Idin irinsu: Kirsimeti, da na Sabuwar shekara da makamantansu, duk waɗannan idi ne na wasu addini daban da na musulunci. Hakanan kuma ba ya halatta ga musulmai su yi bikinsu ko su basu kulawa ko suyi murna da su ko kuma su kasance acikin masu yin su.

Ba ya halatta kwata-kwata musulmi ya alaƙanta kansa da waɗannan Idin bukukuwar Yahudawa da Nasara.

Mu Musulmai muna godiya ga ALLAH bisa ni’imarsa da baiwarsa da falalarsa na kasancewar mu acikin addinin musulunci. Don haka ba za mu taɓa yin murna da Idin Kiristoci ba. Saboda mu Musulmai ne.

Kuma Manzon ALLAH (ﷺ) Ya umurce mu da saɓa musu acikin al’adunsu da ɗabi’unsu

Don haka mu Musulmai mun godewa ALLAH bisa ni’imar musulunci da sunnar Manzon ALLAH (ﷺ)

MURNAR KIRSIMETI HARAMUN NE.
Post a Comment (0)