MAI MUTU’A, MATANKA NAWA?

MAI MUTU’A, MATANKA NAWA?  


Amsa ta gaskiya, tsakani da Allah, ita ce: Ba iyaka! ƴan Shi’a sun ruwaito daga Imaminsu na biyar, Abu Ja’afar, ya ce: “Mutu’a ba da mata huɗu ba ne kawai; domin ita (mace mai Mutu’a) ba’a sakin ta kuma ba ta gado, ba’a gadon ta. Ita mai jinga ce kawai.” [Abu Ja’afar Muhammad binul Hassan Aldusi, Al’istibsar Fi Ma Ikhtalafa Minal Akhbar, bugun Darul Kutubil Islamiyya, Tehran-Iran, 1390 B.H., muj. na 3 shafi. na 147]. Har yau, sun ruwaito daga Imaminsu na shida, Abu Abdillahi, cewa an tambaye shi dangane da Mutu’a: Ana iyakance ta da mata hudu? Sai ya ce, “Ka auri dubu; su ƴan jinga ne kawai.” [A duba Al’istibsar na Aldusi, muj. na 3 shafi na 147; da Tahzibul Ahkam shi ma na Aldusi, muj. na 7 sha. na 259].    
 
LUWAƊI DA MATA  
Malaman Shi’a ƙazamai suna halasta yin luwaɗi da mata kuma suna dangana halaccin wannan ta’asa ga Imamansu a bisa ƙarya. Sun dangana haka ga Imaminsu na shida, Abu Abdillahi Ja’afar Sadiƙ. Suka ce wani almajirinsa mai suna Abul Ya’afur ya ce, “Na tambayi Abu Abdillahi (AS) dangane da halaccin mutum ya zakkewa mace ta duburarta. Sai ya ce: Babu laifi idan ta yarda.” [A duba Al’istibsar na Aldusi, muj. na 3 sha. na 243]. Haka nan sun dangana halaccin wannan ƙazanta ga Imaminsu na takwas, Abul Hassan Musa Rida. [Al’istibsar, muj. na 3 sha. na 243]. 

Uban tafiya, Ayatullahi Ruhullahi Khumaini, yana daga cikin malaman Shi’a masu ganin halaccin al’amarin. Ga abinda ya ce: “Ra’ayi mafi ƙarfi, kuma mafi bayyana, shi ne halaccin saduwa da mace ta duburarta.” Haka nan ya faɗi ba sayawa, ba sakayawa. [Duba littafinsa, Tahrirul Wasila, muj. na 2 shafi. na 241].   

Babu shakka wannan ra’ayi na ƴan Shi’a ya saɓawa Alƙur’ani mai girma inda Allah Maɗaukaki yake cewa, “To idan sun yi wanka (watau matayenku) sai ku je musu daga inda Allah ya umarce ku.” (Suratul Baƙara: 222). Malaman Tafsiri sun haɗu a kan cewa abin nufi da inda Allah ya umarce ku’ shi ne farji, ba dubura ba. Haka nan kuma ya saɓa da hanin Annabi(SAW) inda yake cewa, “Kada ku zakkewa mataye ta duburarsu.” [Tirmizi da Nasa’i da Ibnu Maja duka sun fitar da Hadisin].    

Muna roƙon Allah Maɗaukaki ya tsarkake mazan al’ummar Annabi da matanta daga wannan ƙazanta ta Majusawa.          
 
ARON FARJI   
Manyan malaman Shi’a suna halasta aron farji. Sayyid Hussain Musawi ya yi bayanin ma’anar aron farji kamar haka: “Aron farji ma’anarsa shi ne mutum ya bayar da matarsa ko baiwarsa ga wani mutum dabam sai ya halasta gare shi ya ji daɗi da ita ko kuma ya yi duk abinda ya ga dama da ita. Idan mutum ya yi nufin tafiya sai ya bar matarsa a wajen maƙwafcinsa, ko abokinsa, ko kuma duk mutumin da ya zaɓa, sai ya halasta a gare shi ya yi abinda ya ga dama da ita a tsawon tafiyar mijinta.” [Sayyid Hussain Musawi, Kashful Asrar, sha. na 46-47].    

Don halasta wannan ɓarna, malaman Shi’a suna dangana ruwayoyi ga Imamansu a bisa ƙarya. Daga cikin irin waɗan nan ruwayoyi, akwai abinda suka dangana ga Abu Abdullahi. Alɗusi ya karɓo daga Abul Hassan Aɗɗari’i, ya ce: “Na tambayi Abu Abdillahi (A.S) dangane da aron farji, sai ya ce: Babu laifi.” [A duba Al’istibsar na Aldusi, muj. na 3 sha. na 141]. Har yau, Alɗusi ya karɓo daga Zuraratu, ya ce: “Na tambayi Abu Ja’afar (A.S) dangane da mutum ya halasta wa ɗan uwansa farjin baiwarsa. Sai ya ce: Babu laifi; abinda ya halasta masa daga gare ta ya halasta gare shi.” [Al’istibsar, muj. na 3 sha. na 136]. Babban malamin Hadisi a wurin ƴan Shi’a, wanda suke ɗaukar sa kamar yadda Ahalus Sunna suka ɗauki Imam Bukhari, watau Muhammad binu Ya’aƙub Alkulaini, shi ma ba’a bar shi a baya ba. Ya ruwaito cewa, Imaminsu na shida Abu Abdillahi Ja’afar Sadiƙ, ya ara wa almajirinsa, Muhammad binu Mudarib, wata kuyanga a lokacin da ya ziyarce shi. Ga abinda almajirin yake cewa: “Abu Abdullahi (A.S) ya ce mini: “Ya kai Muahammad, riƙi wanan baiwa ta yi maka hidima kuma ka shafe ta (ka sadu da ita). Idan za ka tafi, sai ka komo mana da ita.” [A duba Furu’ul Kafi na Kulaini, muj. na 2 sha. na 200].   

Duba ka gani ɗan uwa mai karatu, Allah ya tsarshe ni tare da kai daga sharrin ƴan Shi’a da ɓatansu, yadda Rafilawa suka kai matuƙa wajen ƙoƙarin yaɗa lalata da alfasha a tsakanin al’umma ta hanyar halasta zina da ƙira ƙarya a dangana ta ga zaɓaɓɓun bayin Allah.    
Mu imaninmu shi ne, wannan ruwaya da aka dangana wa Ja’afar Sadiƙ ƙarya ce aka yi masa. Imam Ja’afar Sadiƙ ba zai bar tafarkin kakansa Annabi(SAW) ba, ya bi tafarkin Majusawa.  
 
Muhimmiyar Sanarwa  
Dukkan littafan malaman Shi’a da muka yi amfani da su wajen rubuta wannan taƙaitaccen littafi ana samun su a laburaren cibiyar Markazus Sahabah dake Sakkwato Birnin Shehu, kuma mai son ya ga waɗannan littafai yana iya yin haka ba tere da wata matsala ba. Laburaren buɗe take ga kowa da kowa.

 
- *JERIN LITTAFAN SHI’A* NA 4: "Auren Mutu’a a wajen Ƴan Shi’a" - na Prof. Umar Labɗo

✍ AnnasihaTv

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

Call/WhatsApp: 08142286718

Twitter: https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)