TARIHIN DUTSEN WASE.
Amsar tambayar; Yusuf Jibril Umar.
Dutsen Wase yana ɗaya daga cikin Duwatsun da suke alamta ilimin tarihin ƙasa a Duniya, wanda a yanzu ba kasafai ake samun makamancin sa ba.
A yadda ilimin tarihin kasa ya bayyana, Duwatsu kamar Goron Dutsen Wase, suna assasuwa ne, sakamakon Dutsen da ke fitad da wuta idan yayi amo daga karkashin ƙasa, sannan ya dasƙare a saman ƙasa.
Wannan amon dutsen da ya assasa Dutsen Wase, yana da dankon sosai, wannan dalilin yasa, bai zube zuwa wuri mai nisa ba, daga inda ya fito, kafin ya dasƙare.
Dutsen Wase a kumbure yake, yayi doro da tsawo sosai daga kan ƙasa, hakan yasa a ƙasarsa akwai gangara sosai. Bisa wannan zubin halittar, ya kasance ɗaya daga cikin kyawawan duwatsu biyar, ire-iren sa, da muke da su a faɗin Duniya.
Ƙananan ramuƙan da ake iya hangowa a jikin dutsen, sun samu asali ne tun lokacin da dutsen yake ƙoƙarin dasƙarewa, sai iska tayi ta shiga cikin sa, har ta haifar da waɗan nan ramukan. Domin ruwan dutse, yakan ba wa iska damar shigar sa. Waɗannan ramukan sun zama masauki ko ince Sheƙa ga wasu nau'in tsuntsayen da suke tasowa daga gabashin Afrika, ana kiran sunan tsuntsayen da "Kwasa-kwasa". Sun mayar da ƙarƙashin dutsen wurin koyon su. Mutanen Wase, sukan yi wa waɗan nan tsuntsaye kirari da " Kwasa-kwasa dama ruwa, Maƙorin ka ba".
Goron Dutsen Wase, daga kan ƙasa, yana da tsawon mita 176 (daidai da taki 577) koma ya fi haka, sannan daga saman Teƙu yana da tsawon mita 426 (daidai da taki 1,398). Tun daga nesan mil 25 (wato kilomita 40) ana iya hango shi saboda da tsawon sa.
An ce, da can, Ƙabilar Jukun (Musamman na garin Kumbur) sun mayar da ƙarƙashin dutsen wurin ɗabbaƙa al'adar su, har sai da suka samu Taƙarda daga gwamnatin jihar Plato, a sheƙarar 1972, tana umurtar mutanen Wase da cewa, yankin ƙarƙashin dutsen, a bar shi a matsayin wurin shaƙatawa da kuma samun kuɗin shiga ga gwamnati. Gwamnati ta ƙatange akalla filin da yakai tsawon hekta 321 don shaƙatawa da kuma kiyon dabbobi.
Yanayin iska da kuma ayyukan halittu, (kamar tafiyar dabbobi, hawan mutane da kuma shawagin tsuntsaye) sun haifar da ɓallewar wasu sassa daga jikin dutsen zuwa ƙarƙashin sa.
Idan za ka kalli dutsen daga nesa, za ka ga tamkar ya rabu gida biyu. Sai dai bai rabu, amma masu ilimin duwatsu (Geologist) sun yi amanna da cewa, akwai lokacin da zai zo, yanayin zaizayar duwatsu da kuma yawan ɓaɓɓakewar da yake yi, zai tilasta wa ɗaya yankin faɗiwa kasa.
A zubin halittar dutsen yana da ma'adanai mabanbanta, wanda sun ƙaƙƙasu sakamakon ɓarewa, ɓaɓɓakewa da kuma ferewar da saman dutsen yake yi, da kuma yawan zaizayar kasar da ake samu a ƙarƙashin sa, wanda ya tilasta masa kasance wa cikin zubin da yake yanzu.
AMAFANIN DUTSEN WASE.
Musamman ga Mutanen Wase da kuma ƙasar Wase gaba ɗaya. Dutsen Wase yana amfani masu yawa, daga cikin su, akwai:
1. Wurin Shaƙatawa.
Ƙarƙashin dutsen Wase wurin shaƙatawa ne me ban ƙaye, inda maza da mata, yara da samaruka, sukan haɗu domin nishaɗin ɗaukar hoto, sada zumunci da kuma bukukuwa. Ta wannan hanyar gwamnati tana iya samun hanyar kuɗin shiga matuƙa.
2. Ilmantarwa.
Dutsen Wase yana bayar da wani ɓangare na tarihin ƙasar Wase, da kuma tallafawa binciken ƴan makaranta, da kuma tarihin ƙauyukan da suke kewaye da garin Wase.
3. Garkuwa.
A lokuta da dama, musamman a sheƙarun da suka shuɗe, Dutsen yana zama garkuwa ga mutanen Wase, ta hanyar ba su mafaka daga farmakin magauta. Wanda yake yiwa magauta wahalar ketarawa ta saman dutsen don su riski mutanen Wase.
4. Ma'adanai.
Wannan Dutsen yana samar da duwatsun da ake amfani da su wurin gina titi, magudanar ruwa (Lambatu), Gadoji da kuma gidaje. Hakan ke bawa mukusantansa ayyukan yi. Kuma yana kunshe da wasu albarƙatun ƙasa.
5. Haɓɓaka Noma.
Manoma suna amfani da ƙarƙashin dutsen wurin noman Masara, Dawa, Shinkafa, Tumaturi da sauran su.
6. Muhallin Dabbobi.
Wasu daga cikin dabbobi musamman Birrai da Gwaggo da kuma tsuntsaye musamman Kwasa-kwasa, da kuma kwaruna, suna samun muhalli a cikin ramukan da ke jikin dutsen.
ANA HAWAN DUTSEN WASE?
Eh tabbas! Ana hawa.
Ga wani labari mai ban tausayi da aka yi a Wase daf da Turawa sun kusa zuwan kasan nan. Da, kafin turawa su zo, ita Wase tana cikin kasar Bauchi ne.
To, a Wase akwai wani irin makeken dutse tirim, wanda har daga wurare masu nisa ana hangen tashinsa sama. Daga can sama kuma sai dutsen ya zama falale, ya baje ya zama kamar an masa lebur. Ba abinda ake gani kansa sai tsuntsaye iri-iri. Daga angulai, sai maiki, sai shirwoyi, sai hankaki sun fi gaban a kirga. Kai, wannan dutsen da girma yake, tirkashi! Ga shi dai gungurun, ya cika gaba, sa'annan dab da shi ba komai, ba kuma kowa, shine ya zama kamar garkuwan garin nan wase. Akwai labaru masu ban tsoro da a ke fada game da dutsen nan.
A zamanin da, babu mai ko tsayawa kusa da dutsen nan. To watarana sai wadansu mutane, su biyu, su kayi kisan kai, aka zartar da hukunci (su ma za a kashe su). Aka tafi da su kurkukun Bauchi.
Don a tabbatar ko ana hawan dutsen nan na Wase, ko ba shi hawuwa, kuma gani shin me ke samun mutum idan ya haushi, sai aka tura mutanen nan biyu da aka musu hukuncin kisa, sarki yace idan sun hau dutsen nan ba za a kashe su ba.
Da jin wannan dama da aka ba su, sai mutanen nan suka yi ta murna. Suka ce sun yarda za su jarraba hawansa. Takanas aka taho da su daga Bauchi, aka kawo su har gindin dutsennan, don su hau a ga abinda zai auku gare su. Ajiyan Bauchi ma shine ya taho da mutanen nan, ya kawo su gindin dutsennan yace musu, to, bismilla.
Jiki na rawa, suka fara. Daya daga cikinsu har ya kusa cin rabin hawa, sai ya su6uto, yayi irin fadowan nan da kadangare ke yi, rim. Nan take ya karairaye ya mutu. Dayan kuwa yayi ta kokari har ya akai sama can koli. Kowa ya ganshi a sama. Amma fa sai saukowar ta yi masa wuya. Idan ya dubo ya ga yadda kasa take da nisa, sai ya rasa abinda yake masa dadi a duniya. Daga karshe dai ya haukace a can sama. Saboda tsananin kishin-ruwa da yunwa. Hakan yayi sanadiyar mutuwarsa.
Wasu sunce, kasusuwansa ya jima a saman wannan dutsen.
Kwatankwacin hakan ya faru, shekaru 4 da suka gabata.
Rana, 24-03-2018, rana ne da zai yi wuya ga jama'an Wase, su mance da ita, rana ce da za'a sakata a cikin kundin tarihin Wase. Rana ne wanda aka dauki sama da shekaru 20 ba ayi irin ta ba. Rana ne da kowa ke farin ciki da alfahari da ita. Rana ne da jarumai suka nuna kwazonsu.
Duk da tsoron da ake wajen kusantar dutsen a shekarun baya, amma an kawar da wannan tsoron, ta yadda, yara kanana, maza da mata, tsofaffi da samaruka, 'yan gari da 'yan kauye sun halarci wurin taron da aka gudanar wanda sanadin hakan yasa aka hau kan dusten. (ko da yake anzo da shirin hakan).
Idan aka kasa dutsen kashi uku (3), akalla mutane sama da goma (10) sun samu nasarar hawa kan kololuwar dusten, inda suka daga rigar su kamar yadda ake daga tuta yayin yaki. Wadannan sune wadanda bayanai suka nuna cewa, an musu babban kyauta, kuma mai tsoka, sannan daya daga cikinsu ya rasa ransa, lokacin da yake kokarin sauka.
Kashi biyu-cikin-uku (2/3) na dusten, wadanda suka samu daman halartar taronne suka iske wurin, wanda mafi akasarinsu matasa ne maza da mata sannan kuma yara, wasu sun hau ne domin tuntuni suna da muradin haka, wasu kuma sun haune domin su dauki hotuna, da dai sauran manufofi.
Kashi daya-cikin-uku (1/3) na dutsen ma haka yake, cike da matasa maza da mata yara da manya, wanda nima anan na tsaya, na dauki hotuna. Wasu tsoro ya hana su hawa, yayin da wasu kuma dama iya nan suke son tsayawa.
Wannan taron yayi armashi sosai, wanda ke wajen wase, kuma dan Wase ne shi, ya jiza yasta matuka. Wanda kuma yake jin labrin dutsen ko yake ganinta a hoto, lamarin zai bashi sha'awa musamman idan yaga hotunan hawan dutsen.
Allah ya karfafa mana garin mu.
© Prof. Sufyan