A CIKIN MUTANEN NAN, A WANE RUKUNI KAKE?

A CIKIN MUTANEN NAN, A WANE RUKUNI KAKE?



Samari 3 sun je "Interview".Shugaban kamfanin sai ya ce musu " 2 + 2 = 5 "!!??

Sai na farko ya ce, tabbas haka amsar ta ke ran kai daÉ—e.

Na biyu ya ce, ran kai daɗe in muka ƙara ɗaya 1 amsar zata zama 5.

Na uku ya ce, ran kai daÉ—e amsar ba daidai ba ce, 4 ita ce daidai.

Bayan kwana 2 sai aka kafe sakamako, na 1 da na 2 sun ci amma na 3 ya faÉ—i.

Mataimakin Shugaban Kamfanin da ya ga haka, sai ya tambayi Shugabansa, ya haka? bayan na 3 shi ya amsa tambaya daidai...!!!

Shugaban ya ce: Na 1 maƙaryaci ne, kuma ya san shi maƙaryaci ne amma yana son abin da zai burge mu, irinsu abin buƙata ne a wurin aiki.

Na biyu ya yi amfani da ƙwaƙwalwarsa, shi ma abin buƙata ne. Na 3, mai gaskiya ne, kuma ya san akan gaskiyar sa yake, ba zai canza ba, irinsu suna bamu wahala wajen aiki.

Ya kalli mataimakinsa ya ce, in ka fahimci abin da nake nufi, shin 2 + 2 = 5?

Mataimakin ya ce, ran kai daɗe bayan na saurari bayananka; mutum mai ƙaramar ƙwaƙwalwa kamar ni ba zai iya amsa tambayarka ba.

Shugaban sai ya ce, irin nau'inku su ne munafukai, kuma muna ƙaunar aiki da ku...!!!

Ba'asi : wannan shine Halin da muke ciki a kasar nan.😭😭😭

DAGA SHAFIN MALAM IBRAHIM MUSA.
Post a Comment (0)