AIKI YA FI AURE

Aiki yafi aure... 
~~~~


Innalillahi wa inna ilaihi rajuun. Yan uwa wata masifa ta shigo gidajen mu tana lalata mana gidajen mu, kuma tana lalata rayuwar ƴaƴan mu. A yau mun wayi gari mutum yana da mata suna zaune lafiya, da zarar ta samu aiki, sai ta ɗora buri, taja dinga, ta dauka cewa yanzu yawon zuwa wajen aikin ta yafi auren ta da yayan ta. 

A yau sai kaga mace na aiki a wancen garin, shi kuma miji yana wani garin. Ko kuma shi miji yana aiki amma matar sa baza ta iya hakuri ta tabishi don su zauna tare. Wai saboda gurin bai mata ba, ko kuma ya mata nisa. At times sai matar ta zabi rabuwa ko kashe auren don kawai tayi aiki ko don ta zauna a garin da take so. Toh don Allah duk gatan ki ko darajar ki, kin kai Nana Aisha ne ko Fadhima ƴar Manzon Allah? Gidajen su ko kitchen din gidan ki basu kaiba, kuma ranar Qiyama sune a sahun gaba wajen shiga Aljannah. ☺ 

Ko kuma idan ta kafu akan wata sana'a da take yi sai ta ma fara jin cewa yanzu tafi karfin zaman aure, sai yadda take so haka za'ayi. Sai ta rika ganin auren is secondary and neman duniyar ta is primary. Wata har fada tayi, "Ni fa kar kayi tsammanin zan baka lokaci, neman kudina zan sa a gaba". Kuma unfortunately, iyaye yanzu sun yi biris da ido basa daukar matakin da ya dace. Sai suce wai kanawa ƴarsu hassada ko bakin ciki. Wata uwar ma cewa tayi "Toh zata rika yawo da shi a jakane, ko nono yake sha". Kaji fa don Allah. 🤦‍♂️

Wannan ya sabawa addinin mu da al'adun mu na kasar hausa. Yana da kyau mace ta sani, ba dole bane, ba hakkin ta bane tayi aiki ko neman kudi, alfarma ce, it is a privilege not an obligation. Hakkin mijin ta ne ya mata hidima, ya kula da ita. Domin lokacin mijin ki ne kike shiga a duk lokacin da kika fita don neman kudi ko aiki. Kuma hakkin sa ne, kudin salary din ki, shima hakkin sa ne, domin lokacin da ya kamata ki bashi ne kike bayar wa a waje. 🤷‍♂️

Wannan sabon salo ya kara yawaitar baraka a gidajen mu, sannan hakan yana kawo mutuwar aure. Haka zalika, duk tsoron Allah mutum ko mace ko namiji, sai mutum yaji sha'awar yin wani abu da ya sabawa shariah, ko dai zina, ko kuma shashanci da outside partners. Especially Maza, wannan yafi affecting na su. Duk inda aka ce namiji na zaune ba tare da iyali ba, sai kaga ya dauki wasu halaye na banza, wanda a karshe sai sun zamo wani sila na lalata masa rayuwa da kuma rayuwar yayan su. Sannan idan yace zai kara aure bala'e salamu alaikum. 🙆‍♂️🙅

Yan uwa na mata, zaman ku tare da mazajen ku shine mafi alheri a gare ku har a gurin Allah. Wannan sabon raayin, yahudawa ne suke yi, shi yasa suke fasiqanci ba birki. Ba'a hana ku aiki ba, ko sana'a, amma a baiwa komai hakkin sa. Tarbiyyar yaya yanzu ta koma wajen house girl da creche. Iyaye sun daina zama a gida, kullum mace tana kan titi, miji a wahala, yaya a wahala. Kuma abin haushi shine, ita idan ta fita ta samo, still mijin shi ne yake komai. Aure sacrifice ne. Dole ne ki zauna kusa da mijin ki, dole ne ki kula da gidan ku. Haka iyayen mu su kayi, kuma da haka ne suka zauna lafiya. 

Astagfirullah! Da yawan ku duk da kuna fita aiki, ko kuna kin zama da mazajen, wallahi baku da kwanciyar hankali, Allah ya zare muku ita. Idan kasuwanci ne sai kiga duk samun ki amma ba albarka. Allah ya zarewa abin aminci saboda ba a cikin dadi ake yi ba. Wallahi, duk macen da tabi son duniya, tayi sacrificing auren ta, mijin ta, da yaran ta, wallahi sai taga ba daidai ba. Kuma things will never be alright. Aure ibada ne. Dole a kula da shi. Sai kaga mace duk ta lalece, ta rame, ta yamishe, babu natsuwa, babu kwanciyar hankali. Masu zaman a gida sai ka gansu masha Allah. 😇

Ku kuma iyaye, ƴayan ku amana ne a wajen ku, dole kuyi aikin ku. Allah zai tambaye ku akan irin rawar da kuka taka. Don yarinyar ku tace ita kaza take so, ko kaza zatayi, dole ku dawo da ita kan hanya. Idan ku kayi akasin haka, a karshe zaku kashe auren, kuma wallahi, kun cuce ta, za tayi danasani a lokacin da bazai amfane ta ba. Kuma kun kara yawan zawarawa a waje, and eventually zinace zinace zasu yawaita. Mai magana na cewa "Kowa ya bata ya sani, kowa ya gyara ya sani".

Allah yasa mu dace.
Assalamu Alaikum.
© Muhammad Ubale Kiru.
Post a Comment (0)