ALJANNAR DUNIYA CE, AMMA MAI HANKALI KE GANE HAKA.

ALJANNAR DUNIYA CE, AMMA MAI HANKALI KE GANE HAKA. 


🍒 Shaykh Ibnu Baaz Allah ya kara rahama agareshi yana cewa "Kayi dubi zuwa ga wanda ke kewaye da kai, gaba da baya, dama da hagu, zaka ga mafi yawan mutane sun kau da kai daga wannan ilmin, sun shagaltu da abunda bai kaishi ba, sun shagaltu da neman duniya suka dukufa akanta har tayi tasiri azukatansu ta shagaltarsu daga komai. 
 🍒 Dan haka kai (dalibin ilmi) ka godewa Allah da bai sanyaka daga cikin irin wadannan ba, baka cikin wadanda duniya ta shagaltarsu daga barin lahira ba, ka godewa Allah da ya kubutar dakai daga wadannan abubuwan, hakika wannan ni'imace mai girma da Allah ya maka ya kuma shiryar dakai, ya yassare maka hanyar neman ilmi mai amfani, akullum kana sauraron Allah yace Annabi yace. Tabbas yaku yan uwana wannan itace Aljannar duniya amma mai hankali kadai zai gane haka".

مجموعة رسائل العلامة ابن باز ٣٣٦

#Zaurenfisabilillah 

Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)