DUNIYAR MUTUWA // 03

DUNIYAR MUTUWA // 03

.


Chan sai ga wani mutum ya zomin cikin tsananin duhu da nake gani, yazo min da Gemuna fari fat, ya ce da ni: Yaa kai Daana, wannan itace qarshen rayuwarka, kuma na zo maka ne ina mai maka nasiha kafin kaz,,,,,,,x ذى رؤى ذى, hadu da Uban-gijinka, Haqiqa na san ka, kai mutum ne mai hazaaqa, kana son Alkhairi, don haka da sannu zan maka wasiyya da wata wasiyya, domin Allah ne ya aiko ni wajenka.
.
Sai na ce: menene kake so? Sai ya ce: Ka ce: “Na yi Imaani da Cross”, domin na rantse da Allah shi ne kubutarka, idan kai Imaani da shi zan maisheeka ga iyaalanka da yaaranka, sannan in mayar maka da ranka, ka fadi haka da sauri, bamu da lokacin tsaiko! Na san wannan shi ne Shaidan, duk da irin radadin da nake fama da shi na fitar raina, ban gushe da Yarda ga Ubangijina ba da Annabina S.A.W.
.
Nace masa: Maza juya ka ba ni waje ya maqiyin Allah, haqiqa na rayu musulmi, kuma da izinin Allah zan mutu akan haka. Sai Fuskarsa ta chanza ya ce: Ka saurare ni, baza ka kubuta ba a yanzu face ka mutu banasare ko bayahude, in kuwa kaqi, zan qaara maka radadi kuma in dauki ranka. Na ce: Rayuwa da Mutuwa duk suna hannun Allah ne, ba a hannunka ba, ni bazan mutu ba sai a kan Musulunci, sai fuskarsa ta yamutse, shaidaanin ya ce: idan ka fitine ni (kaqi bin umarnina) to Daruruwanka baza su iya ba!
.
Kuma ya ishe ni tunda na iya sanyaka kana saabawa Allah da yawa, kuma kana keta iyakokinsa. Sai naga ya kalli sama, kamar ya hango wani abu da yake tsoro, sai ya gudu da sauri, sai nai mamakin saurin wucewarsa, kuma nai mamakin menene abin da ya tsorata shi haka! Ban dauki wani lokaci ba, sai naga wasu fuskoki baaqi agare ni masu girman Halittaar jiki sun sauko a gare ni, suka ce min: Assalaamu Alaikum.
.
Na ce: Wa’alaikumus-Salaam. Sai su kai Shiru ba su ce komai ba, tare da su akwai Likafani, sai na san wannan ita ce qarshe ba makawa, sai wani malaa’ika mai matuqar Girma ya sauko, ya ce: “Yaa ke rai natsatstsiya, ki fito zuwa ga gaafara daga Allah da Yarda. Wallahi sai na ji aminci wanda ba zan iya misaltawa ba a sanda naji wannan kalmah daga gare shi, nace masa: Bushaararka ya Malaa’ikan Allah!
.
Sai ya cire raina, na kasance tsakanin yanayin barci da Haqiqa, na ji Tamkar ina miqewa daga jikina ina hawa sama, na waigo qasa sai naga jikina mutane sun dabai-bayeshi, sun sanya mayaafi akan jikina, ina ji wasunsu na cewa:
.
Innaa lillaahi wa innaa ilaihi raaji’un!
Naga Tamkar Malaa’iku 2 sun dauke ni sun sanya ni cikin likafanin cikin sauri, sun daga sama da ni, ina waiwayawa daama da hagu, na hango rufin sama chan nesa, ahaka suna qaara dagaawa da ni, muna keta giraagizai, tamkar ina cikin jirgi, har na soma ganin mutane qananaa-qanaana a qasana, sukaci gaba da gudu da ni zuwa sama, har na soma ganin qasa tamkar qwallo qarama, sai na cewa Malaa’ikun:
.
Shin Allah zai shigar da ni Aljannah? Su ka ce: wannan sanin na wajen Allah, mu dai Malaa’iku ne da aka wakilta mu don daukan ran Musulmai kadai. Dukan mu sai hankalinmu ya karkata ga wasu Malaa’iku da muka ga sun zo sun wucemu da sauri, dauke da wata Ruhi mai tsananin Qamshi, inda na shaqi qamshin miskin da ban taba shaaqar tamkarsa ba a rayuwata, na cewa Malaa’iku: Wanene wannan?
.
Ni dai ban da na san cewa Annabi Muhammad S.A.W shi ne qarshen Annabaawa, da na ce wannan Ruhin Annabi ne!  Saboda Rakiyar Malaa’iku da na gani sun mata, da Qamshinta gami da yanda suke riqe da ita cikin Girmamawa da Karramaawa!
.
Allahu Akhbar! Jama’a Kunsan Wannan Gaawar wacece?

# Adam Sani Abu umayra

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)