DUNIYAR MUTUWA // 05
Da muka isa sama ta 2, nan ma aka bude mana har muka isa ta 7, sai na ga ita ce mafi girman sammai, na ga tamkar rafi a gabanmu, na ga Mala’iku sun sunkuyar da kawunansu. Suka ce: “Allahumma innaka antas-salaam waminkas-salaam tabaarakta ya zhal-jalaali wal ikraam” sai na ji wani firgici, na qasqantar da kaina hawaye na zubo min, sai Allah ya cewa Mala’ikun: “Ku sanya littafin bawana cikin illiyin (shi ne rukunin da ake sanya littafan yan Aljannah – Allah ka sanya mu cikin su -), kuma ku mayar da shi zuwa qasa, domin daga gareta na halicce su kuma cikinta zan mayar da su kuma daga gareta zan tashe su wani lokaci na daban. Saboda tsananin firgici, tsoro, da farin ciki da murna, ban iya cewa komai ba.
.
Sai na ce: Tsarki ya tabbata gareka, ba mu bauta maka ba yanda ya kamata! Sai Mala’ikun nan suka sauko da ni zuwa qasa, duk sanda muka hadu da mala’iku sai mu yi musu sallama, sai na cewa Mala’ikun: shin zai yiwu na san abin da ya faru da gangan jikina da iyalaina? Sai suka ce: jikinka dai zaka gan shi, amma iyalanka ayyukan su ne kawai da zasu dinga maka kyautarsu za su dinga riskarka, amma ba zaka gan su ba! Suka dawo da ni qasa, suka aje ni kusa da jikina, suka ce: ka kasance a jikinka, mu aikinmu ya qare a nan, bayan an sanya ka a qabarinka, wasu Mala’ikun 2 zasu zo maka! Sai na ce da su: Allah ya muku albarka, ya saka muku da alkhairi! To amma zan sake ganin ku kuma?
.
Sai sukace: A ranar Qiyaamah zamu tsayu gaba daya, wannan shi ne ranar halatta (domin dukkan Mutane, Aljanu da Mala’iku zasu halacce ta), sai na ga sanda suka ambaci qiyamah sautinsu ya chanza, sannan suka ce: Amma in ka kasance cikin yan Aljannah, zamu zamo tare. Na ce: To bayan na ga Aljannah kuma na ji sautin ababen cikinta, shin akwai sauran shakku agare ni (na zan shiga ko za’a kora ni wuta)? Sai suka ce: lamarin shiga Aljannah lamari ne da Allah kadai ya mallake shi, kuma kai ka samu karramawa saboda ka mutu musulmi, abin da yayi saura shi ne a nuna maka ayyukanka (a qabarinka da qiyamah) da kuma mizani!
.
Sai fuska ta ta chanza har na kusa kuka, domin ina tuna zunubaina tamkar manyan duwatsu! Sai suka ce da ni: Ka kyautata zatonka ga Ubangijinka, kuma ka qudurce cewa Ubangijinka bai zaluntar kowa, sai sukai min sallama, sukai sama da sauri. Na ga jikina a kwance, sannan sai na ji sautin kuka, sauti ne da na san shi, mahaifina ne me qaunata da kuma dan-uwana, -subhaanallah, ina nake ne yanzu?- sai na kalli jikina na ga ana zuba masa ruwa, sai na gane cewar yanzu ana wanke gaawata ne! Sautin kukan nan na matuqar takuramin. Amma duk sanda na ji mahaifina na cewa: “Allah ya sassauta maka, Allah maka rahmah” sai na ji tamkar ana zubamin ruwan sanyi ne, sai suka rufe jikina da farin likafani.
.
Sai na ce cikin raina: KAICONA ACE MA BAN TABA BARIN MINTI 1 BA A RAYUWATA FACE CIKIN AMBATON ALLAH, KO SALLAH, KO WATA IBADAH! Kaicona ace ina sadaqa dare da rana, kaicona kaicona! Babban burina shi ne qabari, da abin da zai biyo bayansa, sai na ji mai min wanka na cewa: shin zaku masa sallah ne bayan La’asar? Babana ya ce: Eh in sha Allah – cikin kuka – Suka dauki gaawata, ina kallon ta amma ba na iya magana ko motsi, suka shigar da ni firij da ake sanya gaawarwaki, chan sai na ji ana cewa: ku dauke shi ku kai shi masallaci! Suka dauke ni ina jin duk maganganunsu, babban abin da ya fi damuna shi ne kukan mahaifina,
.
Kamar in ce masa: Kada ka damu yaa Baba, abin da ke wajen Allah ya fi alkhairi! Don Allah kabar kuka, domin ina shan radadi a dalilin kukanku, amma ko na fadi baza su jivni ba! Ina jin sautukansu kuma ina gane muryar kowa, yan’uwana, kuma duk ina jin maganganunsu! Suka isa masallaci suka aje ni, sukai sallar la’asar, nai kwadayin dama a ce ina tare da su mu yi sallar nan ni ma na samu lada! Chan bayan idar da sallah sai na ji ladan na cewa: Jama’a ku zo mu yi wa dan-uwanmu sallah
Zamu chigaba da yardar Allah...
# Adam Sani Abu umayra
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248