KUSKURENA YA YIN DA NAKE ALWALA 18

*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
                *ALWALA*


🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*FUTOWA TA 👇*
          *(18)*


          *FITSARI A TSAYE*

    Abun da yake na dai dai dan gane da fitsari a tsaye yahalatta, saboda hadisin Huzaifa bn yaman yake cewa Nakasance tare da manzan Allah saw sai muka isa bolar wasu mutane sai manzan Allah saw ya yi fitsari a tsaye, sai na matsa baya sai manzan Allah saw yace dani na matso sai na matso har na qarasa kusa da duga dugansa sai ya yi Alwala kuma ya shafa akan kuffinsa. 
    Amma abun da ibn maja ya rawaito cewa manzan Allah saw ya hana mutum ya yi fitsari a tsaye, acikin ruwayar akwai Adiyyu bn fadlu kuma shi matrukine hadisinsa ba karbabbe bane. Haka zalika Abun da aka rawaito daga ummuna Aisha cewa "Duk wanda ya baka labari cewa manzan Allah saw ya yi fitsari a tsaye kada ka gasgatasa, bai kasance yana fitsari ba sai a tsugunne "wannan shima hadisine ingantacce kamar yadda na huzaifa yake sai dai zamuce ummu Aisha tana fadane dan gane da Abun da manzan Allah saw yake yi acikin gida wanda idonta yake kaiwa kai amma abun da ya shafi waje wannan bata da ilimi akansa shi kuma huzaifa ya fita saninsa, kenan zamuce acikin gida manzan Allah saw bai taba yin fitsari a tsaye ba, kamar yadda a waje idan dalili yasa yana yin fitsari a tsaye. 
     Haka zalika duk kan wani hadisi da yazo yana hana yin fitsari a tsaye bai ingantaba kamar hadisin Umar bn khaddab yake cewa manzan Allah saw ya ganni ina fitsari a tsaye sai yace ya umar kada ka sake fitsari a tsaye, sai yace bayan wannan maganar ban sake fitsari a tsaye ba. Shima wannan hadisin bai ingantaba saboda akwai ibn abi mukariq shima da'ifine, da hadisin da Umar yake cewa "ban qara fitsari a tsaye ba tun lokacin da na musulunta "da kuma wanda yake cewa "Abubuwa uku suna daga cikin jafa'i fitsari a tsaye, goge fuska kafin mutum ya gama Alwala da bushe gurin da zakayi sujjada "duk kan wadannan hadisan basu ingantaba. 
   Yin fitsari a tsaye ya tabbata daga gurin Umar bn khaddab, Abu Huraira, zaid bn sabit, Abdullahi bn Umar, Sahal bn sa'ad, Anas bn malik, Aliyu bn Abi dalib, bn sirin, urwata bn zubair, bn munzir yana cewa fitsari a tsugunne shi yafi soyuwa agareni, Amma yi a tsaye ya halatta duk kaninsu sun tabbata daga manzan Allah saw , haka zalika an hakaito daga khaddabi da baihaqi da wasunsu daga Imam Abu Idris Ashshafi'i cewa :"larabawa sun kasance suna yin maganin ciwan baya ta hanyar yin fitsari a tsaye. 



*ALLAH SHINE MASANI*


🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*MU HADU A FUTOWA TA 19*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
          *(Abu Rumaisa)*
        🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)