DUNIYAR MUTUWA(7)


DUNIYAR MUTUWA(7) 


Bayan wucewarsu (Munkar da Nakir) sai na soma jin wani zafi a qabarina, jikina ya soma makyarkyata, naji tsoron kada ace qofar wuta aka bude sabida tsananin zafi, amma ba abinda nake ji illa tsananin zafi wanda ke fitowa daga jikina.
Chan sai wasu Malaa'iku 2 sukazo min, sukace: Assalaamu Alaikum warahmatullahi wabarakaatuhu.
Nace: Wa'alaikumus-salaam warahmatullahi wabarakaatuhu.
Sukace: Mu malaa'ikune, munzo nuna maka aikinka a qabarinka, da kuma tattara kyawawan ayyukanda ake maka kyautarsu daga nan Har rananr qiyaamah.
Nace dasu: wallahi tunda na mutu nake ganin ababen tsoro, ban zaci haka abin yake da tsanani ba! Amma zaku amincemin nai maku tambaya? Sukace Eh!
Nace: Shin ina cikin Yan-Aljannah? Bayan duk wannan abubuwa da nasha, shina akwai wani abu da zai iya sanyawa Allah ya saani a wuta?
Sai sukace: Kai Musulmi ne, abinda ya sameka, don kayi Imani da Allah da Manzonsa ne, amam shiga Aljannah ko wuta, ba wanda yasanshi sai Allah, sai dai munaso ka sa aranka cewa: Koda Allah ya sanyaka a wuta, to bazaka dauwama a cikinta ba, domin baka shirka kana kadaita Allah!
Sai na soma kuka nace: To idan Allah ya sanya ni a wuta, kwana nawa zanyi cikinta?
Sukace: ka kyautata zato ga Ubangijinka kawai, kuma ka sani, shi mai karamci ne!
Don haka yanzu zamu soma nuna maka ayyukanka, tun daga sanda ka Balaga har zuwa qarshen numfashinka a inda kukai hatsari!
Kuma zamu soma ne da Sallarka, domin itace bambancin Musulmi da Kafiri!
Amma ka sani, duk wani aiki na qwarai da kayi bazaka ga sakamakonsu ba, domin ayyukanka na qwarai dukkansu a sagale maka su!!!
Sai na ce cikin mamaaki: Me yasa?!! Kuma menene alaqar wannan da Zaafinda nake ji a jikina, wanda nakeji kamar an tattaro zazzabin duniya an taara min ajikina??
Sukace: wannan Nada Alaqa da abinda kakeji, sabida sakacinka wajen biyan baashinda ake binka na kudade da kaayayyaki! Kuma yanzu kana cikin hatsari babba!!!!
Nace cikin kuka: Ya za'ai kenan? Yanzu Baashi shine yasa aka Tsayar da Ayyukana, kuma nakejin wannan tsananin zaafin?
Sukace: Tabbas kuwa!!!


Yan-Uwa sai kuyi tunani ku gyaara kafin lokaci ya qure maku! Mu hadu a rubutu na 8 don jin ci gaban labarin!

# Adam Sani Abu Umayra 

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248

Post a Comment (0)