DUNIYAR MUTUWA // 06


DUNIYAR MUTUWA // 06


Suka dauke ni zuwa Qabarina, suna tafe cikin sauri, ina jin addu’ar da suke min, ina jin Istirjaa’insu (shine fadin: Innaalillaahi wa innaa ilaihi raaji’un), ina jin kukansu da suke yi, ni kuwa ina cikin halin dimuwa da tsoron abin da zan taras, domin yanzu ina tuno zalunci da na yi, da kuma zunubaina, da kuma lokuta da na kwashe cikin shiririta da shirme maimakon bautar Ubangijina, lallai yanayin akwai tsoro!
.
Bayan sun isa qabarina, sai na ji sautuka da maganganu masu yawa, ina jin maganar masu sanya ni a qabarina, ina jin dayansu na cewa “ku matso da shi, ku sako shi ta nan, ku bude hanya……..”, yaa Allaah, abinda ake ba ni labari kuma nake gani munawa wasu, yau ga shi gare ni. Suka shigar da ni qabari, ina jin wanda ya ciro gaawata na cewa ‘Bismillaah wa alaa millahi Rasulullaah’!!
.
Aka soma shirya itatuwa, da kwaba qasa, ana sanyawa a qabarina, kamar na yi ihu na ce: “Kada kubar ni anan don Allah, ban san me Allah ze min ba in kuka barni”, amma ko na fadi baza su ji ni ba! Naga duhu ya soma tsananta, sautin mutane na rarraguwa, amma ana jin qarar takalmansu da tafiyarsu! Ina ji wasunsu suka tsayu a qabarina suna min addu’a, addu’arsu ta zamo debe kewa gare ni kuma ta zamo sassauci ga qirjina, musamman daya daga cikinsu da na ji yana cewa: “Ku roqa masa tabbatuwa domin yanzu ana tambayarsa”.
.
Kwatsam sai qabarin ya soma matsewa, har na ji tamkar za’a matse dukkan jikina ne, na firgita har na kusa fasa ihu, sannan sai qabarin ya dawo yanda yake, chan sai malaa’iku 2 suka baiyana gare ni, cikin sura me ban tsoro, jikkunansu masu girma ne baqaqe, idanuwan manya, idan suka qyafta ido tamkar walqiya, qumbunansu kamar za su tabo qasa, a hannun dayansu akwai Guduma babba, wacce da ace za’a samu babban birni a buga masa ita, da dukkan birnin sai ya rushe! Dayansu yace min: Zauna. Sai na zauna.
.
Ya ce: Waye Ubangijinka? Shi kuwa me gudumarnan ya qwalo min ido.
Na ce: Ubangijina shi ne Allah!
Na kasance ina amsawa cikin kidimewa.
Sai ya sake cemin: Waye Annabinka?
Na ce: Muhammad S.A.W
Ya ce: Meye Addininka?
Na ce: Musulunci.
Sai suka cemin: Yanzu ka kubuta daga fitinar qabari.
Na ce da su: Ku ne Munkar da Nakiyr? Su ka ce: Eh!
.
Da ace baka amsa ba da mun buge ka da wannan Gudumar, wanda sai ka yi ihun da duk Halittu sai sun ji ihunka in ban da mutane da aljanu! In da ace mutane da aljanu za su ji ihun, da sai sun sume saboda tsabar ihunka!
Kuma da sai ka nitse qasa tsawon zira’i 70!
Na ce: Godiya ta tabbata ga Allah da ya kubutar da ni daga wannan, wannan falalar Allah ne shi kadai! Sai suka wuce, bayan wucewarsu, sai na soma jin wani zafi mai ban mamaki, jikina ya soma zufa yana karkarwa!

Zamu chigaba da yardar Allah

# Adam Zamu chigaba

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)