DUNIYAR MUTUWA(8)


DUNIYAR MUTUWA(8)
.
.

Nace cikin kuka: Ya za'ai kenan? Yanzu Baashi shine yasa aka Tsayar da Ayyukana, kuma nakejin wannan tsananin zaafin?
Sukace: Tabbas kuwa!!!
Kwatsam maganata ta yanke, sanadiyar wani haske da ya bayyana gareni daga saman qabarina, haskenda ya shafe duhun qabarina ya haskakashi baki daya, wani irin qamshi mai dadi na fitowa daga cikinsa, ban taba jin daddaadan qamshi irinsa ba! Sai naji Hasken yace: Assalamu alaikum wr wb!
Na amsa masa: Wa'alaikumus-salaam wr wb, waye kai?
Yace: Nine Suratul Mulk (Tabaaraka), nazone don na nema maka rangwame wajen Ubangijinka, domin ka kiyayeni tsawon rayuwarka, kuma Annabinku Muhammad s.a.w ya baku labarin cewa: ina nemawa duk wanda ya kiyayeni kubuta a wajen Allah!
Nace: Maraba dake, surar da na haddace tun ina qarami, nake karantata cikin sallah da cikin gidana, gashi ayau ina matuqar buqatuwa gareki!
Tace: hakane, sabida hakanema nazonan, zanje in nema maka rangwame wajen Allah yanzu, duk wannan tsanani ya sameka ne a sabili da Baashi da ake binka wanda kai sakaci baka biyashi ba, kuma shine ya sanya aka qi nuna maka ayyukanka kuma kakejin zafi a jikinka!
Nace: to yanzu ya za'ayi na kubuta?
Tace: da dayan abubuwa 3 ne!
Nace cikin hanzari: Meye su?
Tace: Kafinda na fada maka wadannan hanyoyi, shin ko ka rubuta baashinda ake binka a takarda, domin magaadanka su biya maka?


Sanda naji wannan kalmar (Magaada) sai naji tsanani a raina, hawaye ya zubomin, domin na tuno dukkan iyaalai na, Mamata, Babana, Mataata, Yan'uwana da Yaarana! Kaicona, me ya samesu a baayana??? Sai na tuno Yarinyata qaramar sanda muke waya take cewa: "Tanaso na kawo mata Cocoa" to yanzu me zasu ce mata in ta tambaya ina nake? Ya rayuwarta zata daawo bayan mutuwata? Mataata me zatayi baayana? Yanzu ta zama #Bazawara kenan? Ya zatayi da wahalhalun Yaarana a bayana???? Nadinga tunane-tunane, hawaye nata zubomin, damuwata nata qaruwa!!!
Sai Tace dani:

 Kaman ka tuno wani abu ko?
Nace: Eh, Na tuno iyaalaina ne, ya zasu kasance baayana!
Tace: Sunada Allah, shi ya Haliccesu yake azurtasu, kuma shine zai jibinci lamuransu!
Sai wannan Magana ta zamo tamkar ruwan sanyi ga mai qishin-ruwa!!
Nai shiruuuu ina tunani!! Sai naji zafin jikina na qaaruwa! Sai nacewa Suratul-Mulk: Don Allah zan iya sanin baashin nawane ake bina?
Tace: Eh, na Tambayi Malaa'ikandake kula da ayyukanka, yace min Riyal 1700 ne: 1000 na abokinka ne da ake kira Abaa Hasan, 700 kuma guntu-guntun bashin mutane ne da kaci aka taara maka!
Nace cikin mamaki: Gutsa-tstsarin bashi?
Tace: Tabbas kuwa, domin kana sakaci da qananun baashi tun taasowanka, baka damuwa dasu balle ka biyaasu, to sune suka tarun maka!


Nace: To na su waye?
Tace: Riyal 5 na mai saida kayan abinci ne, ka sayi kayan abinci wajensa! Alokacin baka da kudi, ya maka magana kace zaka bashi...........haka­ dai tata lissafominsu........­.kudaden masu min wanki.......
Tace: Sabida yanda kuke Raina baashi, yasa da yawanku kukeshana wahala a qabarinku, Annabinku ashe bai gargadeku gameda baashi ba? Kuma ya gaya maku Shahidi dukda girman matsayinsa amma Baashi nasa a tsaida aikinsa?

Nace: Innaalillaahi wa innaa ilaihi raaji'un!! Yanzu menene mafita??? Wlh jikina zai tsints-tsinke sabida azaabar radadi!!!!!



Mu hadu a rubutu na 9 don jin mafita! Sai mu kula mu biya baasussukandake kawunanmu tun da ranmu!

# Adam Sani Abu Umayra

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)