KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 17
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
11. Mu kiyaye matuƙa wajen gaggawar tura saƙonni ko yaɗa wasu bayanai ga duniya, domin dukkan Musulmi na ƙwarai a kodayaushe yana ƙoƙarin tsare mutuncinsa ne don gudun wofantar da kai a tsakanin al'umma. Don haka wajibi ne mutum ya tabbatar da ingancin abubuwan da za su riƙa fita daga gare shi. Sannan ya kiyaye irin mutanen da zai yi alaƙa da su ta hanyoyin sada zumunta na zamani, don gudun kada ya wayi gari dumu-dumu cikin mu'amala da ashararru, masu keta alfarmar mutane, magulmata, masu hassada da dai sauran jinsin miyagu da ke fakewa da kafofin sadarwa don cim ma burin gurɓatattun zukatansu.
.
Matuƙar mutum ya samu kansa a cikin waɗanda ke hulɗa da irin waɗannan gungun miyagu, lallai martaba da kimar da yake da ita za su zube a wajen mutanen kirki, kuma Manzon Allah (S.A.W) yana cewa "Mutum yana tare da wanda yake so ranar alƙiyama". Wanda kuwa ka gina alaƙa da shi, ka amince masa har kake gaggawar karɓar bayanai daga gare shi don yaɗawa gaba, haƙiƙa akwai alamun tarayya tsakaninku. Nuna amincewa da masu soki-burutsu a kafofin sadarwa tamkar nuna soyayya ne gare su, bisa ayyukansu munana.
.
12. Mu kiyaye ƙa'idar Musulunci ta hana yayata ayyukan ɓarna. Ayyukan alheri su ake yaɗawa don koyi a tsakanin al'umma, amma ayyukan ɓarna da fasadi rufe su ake, ana taƙaita yayata su a tsakanin al'umma. Don haka wajibi ne ga masu hulɗa da kafofin sada zumunta na zamani su yi watsi da mummunar aƙidar da ta shahara a wannan fage na rige-rigen yaɗa ɓarna da miyagun ayyukan da fasiƙai ko kafirai ke aikatawa, sannan su ɗauka cikin hotuna, babu kunya babu tsoron Allah, suna watsa su cikin duniya. Duk mutumin da ya ga abokin hulɗarsa ta kafofin sadarwa na tura irin waɗannan bayanai ko hotuna, to tilas ne gare shi ya yi gaggawar cire shi a cikin abokan hulɗarsa.
.
13. Wajibi ne ga mai amfani da kafofin sada zumunta na zamani ya kiyaye kansa daga ƙirƙirar labaran ƙarya don neman cutar da wani ko birge wani. Haƙƙi ne a kan mai hulɗa da waɗannan kafofi ya kasance mai kiyaye duk abin da zai turawa abokin alaƙarsa tare da tabbatar da sahihancin zance ko bayani kafin ya sake shi ga duniya. Domin ƙarya mummunan aiki ce wadda sakamakonta ke jawo zubar da kimar mutum a nan duniya da kuma horo mai tsanani a gobe ƙiyama. A cikin wani hadisi ingantacce, Manzon Allah (S.A.W) Ya ce:
.
"Ina horon ku da yin gaskiya, domin gaskiya na shiryarwa zuwa ga nagarta, nagarta kuwa na shiryarwa zuwa ga aljanna. Bawa ba zai gushe ba yana gaskiya kuma yana dogewa a kan gaskiyar har sai an rubuta shi cikin masu gaskiya. Kuma, ina horon ku da gujewa ƙarya, domin ƙarya tana shiryarwa zuwa fajirci, fajirci kuma yana shiryarwa zuwa wuta. Bawa ba zai gushe ba yana ƙarya, kuma yana dogewa a kan ƙaryar har sai an rubuta shi cikin maƙaryata". {Bukhari da Muslim}.
.
.
Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248