KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 12

KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 12
.


Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa 
.
MATASHIYA
1. Fasahar sada zumunta ta zamani ana sarrafa ta salo-salo a yi amfani da ita, misali hatta masu tallata haja a manyan kantunan zamani, kamfanoni da ƴan kasuwa na hulɗar kasuwanci da juna a cikin sauƙi a saya, a sayar a ɗauko a kawo daga ko'ina zuwa ko'ina a duniya.
.
2. Haka nan masu fasahar zane-zane na gida, ofisoshi da masana'antu, masu ƙere-ƙere, duk na samun aiwatar da aikinsu da musayar fasaha da sanin juna ta wannan kafar sadarwa, da fito da sababbin zane-zane na zamani.
3. Haka nan bankuna da cibiyoyin musayar kuɗi da duk wata hanyar ciniki da musayar kuɗi da kadarori duk suna yi cikin sauƙi ta wannan kafa ta sadarwa.
.
4. Hatta masanan ilmin magunguna, likitoci da ƙwararru a fannin binciken cuta da magani duk suna amfani da wannan kafa ta sadarwa wajen samun ƙaruwar ilmi, sanin masana da mu'amala da ƙwararru a wannan kafar sadarwa na amfani da wannan kafa a yi ritaya da ƙara binciken bil'adama da dabbobi.
.
5. Haka nan sojoji da duk ma'aikatan tsaro, da masu koyar da dabarun zama cikin aminci, da kamfanonin ƙera makamai da duk abin da ya danganci kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya duk na amfani da wannan kafar sadarwa ta zamani don ci gaba da samun nasara.
.
6. Ta fuskar mu'amala ana ƙulla aure da ƙarfafa soyayya da zumunci da juna ta wannan kafa ta sadarwa.
7. Kafofin yaɗa labarai na rediyo, jaridu, da talabijin duk suna haɓɓaka sashinsu da samun ƙarin dabarun zamani a kafar sadarwa ta zamani.

.

Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)