KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 13
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
HUKUNCIN AMFANI DA KAFOFIN SADARWA
DA SADA ZUMUNTA
Addinin musulunci ya shimfiɗawa ɗan'adam dukkan hanyoyin rayuwa, bisa dokoki da hukunce-hukuncen da suke cikin shari'ar Allah. Babu wani ɓangaren rayuwar bil'adama da musulunci bai yi tanadi a kan yadda za a gudanar da shi ba, kama daga ibadun gaɓoɓi (da na zuciya), mu'amalar yau da kullum, har zuwa zamantakewa tsakanin mutane.
.
Allah (S.W.T) yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki:
قل إن صلاتي ونسكي ومحياي ومماتي لله رب العالمين (١٦٢) لاشريك له وبذلك أمرت وأنا أول المسلمين (١٦٣).
"Ka ce: Lallai ne sallata, da yankana, da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai. Babu abokin tarayya a gare shi, kuma da wannan aka umurce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa". Suratul An'am: 162-163.
.
Sai dai kuma, musulunci addini ne da ke ɗauke da dokoki masu fa'ida da maslaha a fagen gudanar da rayuwar ɗan'adam, bisa rahama da tausayi da Allah ke yi wa bayinsa. Daga cikin abubuwan da ke alamta sassaucin Shari'ar Allah, akwai sananniyar ƙa'idar nan da aka gina hukuncin amfani da ni'imomin da Allah ya tanadar ga bayinsa, cewa: "Dukkan wani abin amfanin ɗan'adam halal ne face wanda hukuncin hanin ya tabbata a kansa".
.
Wani abin da ya ƙara tabbatar mana da haka kuma shi ne, faɗin Allah (S.W.T) ga bayinsa cewa ya halicci duniya da dukkan ni'imomin da ke cikinta ne dominsu a inda yake cewa:
هو الذي خلق لكم ما في الأرض جميعا ثم استوى إلى السماء فسواهن سبع سماوات وهو بكل شيء عليم.
"Shi ne wanda ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma ya daidaita zuwa sama, sa'an nan ya aikata su, sammai bakwai. Kuma shi masani ne ga dukkan komai". Suratul Baƙara: 29.
.
Duk da yake kafofin sadarwa da sada zumunta na zamani sun ɓullo ne a ƴan shekarun nan, lallai addinin musulunci ba zai gaza samun tanadin da ya yi wajen shimfiɗa hukunce-hukuncen yadda ya cancanta a tunkari mas'alolin da ke tattare da amfani da irin waɗannan kafofi ga musulmi ba.
.
Domin kamar yadda bayani ya gabata, dukkan abin da Allah (S.W.T) ya horewa bayinsa daga cikin ni'imomin da ke doron ƙasa, an tanade su ne don amfani da jin daɗin ɗan'adam, face abin da hukuncin hani ya tabbata a kansa. Saboda haka musulunci ya amince da amfani da irin waɗannan kafofi na zamani, matuƙar mai amfani da su zai kiyaye ƙa'idojin da aka tanada cikin hukunce-hukuncen mu'amalar sadarwa tsakanin juna da tsarin zamantakewa tsakanin mutane. Akwai hanyoyi da ƙa'idojin da ya kamata musulmi ya lura da su matuƙa wajen amfani da waɗannan kafofin sadarwa na zamanin.
.
Rubutawa:
Chairman Abbati Mai Shago Flg
(Chief of Admin's Headquarter).
.
Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248