KUNDIN MA'AURATA // 04
MISALI
A wani littafi mai suna (Hatta Yabqal Hub p25), sun kawo labarin wata mata, Sumayya, lokacin da ta dawo gida a gajiye, don neman na rufin asiri ita da yaranta, a lokacin tana da buqatar yin hira da maigidanta kan irin wahalhalun da ta sha a waje take cewa "Abubuwa sun runcabe min, ban da wani lokaci na kaina wanda zan dan biya wa kaina buqatun da suka taso min" da bude bakin maigidanta, wato Adil, sai ya ce "Da zan ba ki shawara kibar aikin da kike yi a kamfaninnan kawai, maganar gaskiya ba ki da buqatarsa, da ma za ki nemi aiki a wani wurin da zai yi daidai da zarafinki na gida ya fi miki"
.
Sumayya ta ce "Ni fa ina son aikin, kawai matsi ne ya yi yawa" Adil ya ce "Manta da su! Ki yi abin da za ki iya kawai" ta ce "Ai abin da nake yi kenan... Kai! Na gaji wallahi, ga shi ma na yi wa mamana alkawari ban kira ta ba" ya ce "Kar ki damu, mace ce mai fahimta, za ta fahimce ki" ta ce "Ba ta da lafiya fa, gaskiya tana buqatata kusa da ita" ya ce "Ke kin cika damuwa ne da qananan abubuwa, shi ya sa da wahala ki sami kwanciyar hankali" sai ta fara magana cikin fushi "Ni wallahi ban jin dadin magana da kai, shin zai yuwu wani lokaci ka saurare ni?"
.
Jin haka sai ya ce "To fadi, yanzu ina sauraronki" ta ce "Ina bata lokacina kawai wai ina magana da kai" tun daganan sai ta riqa damuwa ganin ba ya son ya riqa kula da ita, ita tana son su riqa fahimtar juna, su zauna su riqa tattauna abubuwan da suka shafe su, wanda a ganinta wannan ne ma soyayyar amma ba ta yi dace da wanda ya iya ba, shi ma Adil, wato mijin Sumayyan ya kamu da tasa damuwar, don kuwa bai san abin da ya yi mata ba, shi yana ganin yana qoqarin warware mata matsalolinta ne, ita kuma ta dauki fushi ba gaira ba dalili.
.
A zahiri adil bai san dabi'ar matarsa ba, ya dace kafin a kai ga nema mata mafita, a lissafinta, tana son ya ba ta hankalinsa a farko, ya saurare ta tukun, ya jinjina mata a kan aikin da take yi tukun, in ma mahaifiyar tata ce ya biye mata da farko kafin a kai ga abin da yake qoqarin ba ta shawara da shi, ba ita ba mata da yawa in suna ba namiji labari sukan so ya tsaya ya saurare su, ba wai a nema musu mafita ba, sauraron kansa mace tana ganin qarfafa gwiwa ne, da jinjinawa gami da tausayawa, shi ya sa ita in yana ba ta labari takanyi shuru ta saurare shi ta qarfafa masa gwiwa.
.
Amma a nan ba wai namijin ba zai taimaka wa macen ba ne wajen ba ta shawarar da ta dace, maganar ita ce yaushe ya kamata ya fara magana don nuna mata abin da za ta yi, tana son ta ga damuwar a fuskarsa tukun, ko bai nuna ba to ya saurare ta, ya riqa jinjina mata, masamma Sumayya, ya nuna mata cewa lallai tana shan wahala, kuma bai kamata a riqa matsa mata haka ba, bayan ya gama jin abin da take so ta gaya masa kenan, in ta so sai ya fito mata ta wata hanyar don nuna mata abin da ya dace ta yi.
.
YADDA MACE TAKE JIN KANTA
Mace a ko'ina tana daukar soyayya da matuqar mahimmancin gaske, tana kuma sha'awar ganinta da son yin magana a kanta, a kullum tunaninta ya za ta burge, me za ta yi a ce ta yi bajinta a qarshe a yaba mata? Don haka ka zauna tare da ita kuna hira da dararraku da debe haso ya fi mata komai a rayuwa, zai yuwu ta riqacin kaji, ta wanke goma tana tsoma biyar, duk abin da take so a yi mata cikin gaggawa, ko a kaita inda take so, ta hau motoci masu tsada, amma ka riqa ganinta cikin damuwa, har ka yi zaton rashin godiyar Allah ne, ba haka ba ne.
.
Na san mata da yawa wadanda suke samun goma ta arziqi a wurin mazansu, kowa sha'awarsu suke yi, amma ana gaya musu sai ka ga ransu ya baci, in ba ka san abin da yake damunsu ba sai ka zaci maganarka take baqanta musu rai, alhali tunawa suke yi da irin alaqar da take tsakaninsu da mazajensu na rashin zama da jin matsalolin juna, shi yasa dan abu na tasowa sai ka ji ta kira shi da mugu ko maqetaci, ita a lissafinta cutar da ita yake yi, wasu mazan a zahiri sun riga sun gaji a waje wajen neman halas, sun yi ta kazar-kazar, kamanan kamacan don ganin sun samo abin da gida yake buqata, da sun dawo sai kaga hutu kawai suke buqata a daidai wannan lokacin, kodai kallon talabijin koda kuwa abin da ake yi bai dada su da qasa ba.
.
Ko kuma mutum ya dauki waya yana dan latse-latse, a zahiri nan hutu yake yi don jiki da jini, wannan shi ne babban hanyar samun natsuwa a wurinsa, ita kuwa sai ta yi ta jansa da hira, in ya ri biris da ita sai ta dauka wulaqanci ne, in ba a kai hankali nesa ba wata rana sai ka ga an fara sa-in-sa, masamman ma da yake wasu matan abin farko da za su fara da shi shi ne matsalolin cikin gida, da kuma abubuwan da gidan yake buqata, in ya kasance buqata ba ta biya ba, ko bai da isasshen kudi sai ka ga an sami wani tashin hankalin, da kamata ya yi ta ba shi lokaci ya sarara, ya ci abinci ya natsa, in ta so sai daga ba ya in ta ga sarari ta bijiro masa da maganganun da take so.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248