LABARI »»» 03
AN YI WA ƁERA KIDNAFIN
Wani shahararren malami mai suna Abubakr Muhammad bnu Ahmad wanda aka fi sani da Ibnul Khadwibah (ya rasu 489H) ya hakaito wani abin al`ajabi da ya faru da shi.
Ya ce: "Wata rana ina zaune da daddare ina kwafar rubutu a dakina sai ga wani katon bera ya fito daga rami, can sai ga wani ya sake fitowa.
Sai berayen biyu suka yi ta wasa da tsalle-tsalle, har suka zo jikin fitila kusa da ni.
Lokacin da dayansu ya matso kusa da ni sosai sai na dauki wata tasa da ke gaba na na kife shi da ita.
Da dayan ya ga haka sai ya sheka a guje ya shige rami.
Can bayan wani lokaci sai ga shi ya dawo da dinare daya a bakinsa, ya zo ya jefar da shi a gaba na, sannan ya tsaya yana kallo na.
Da ya ga na ki kula shi, sai ya koma cikin rami ya sake dakko wani dinaren ya zo ya jefar gabana, ya tsaya yana kallo na.
Haka ya yi ta yi daya bayan daya har sai da ya kawo dinare hudu ko biyar (na manta takamaiman adadin).
Da ya ga ban da alamar sakar masa dan uwa, sai ya koma rami ya dakko wata `yar karamar jakar fata ya zo ya aje ta kan kudin da ya kawo, alamar dai kudin sun kare.
Da na ga haka, sai na daga tasar da na kife dan uwan na sa, sai suka yi tsalle baki daya suka shige rami. Ni kuwa na kwashe wannan kudi dama iyali na suka cikin bukata, na je na biya musu bukatar su."
(Mu`ujamul Udabaa`i 5/ ٢٣٥٧)
Da ace `yan kidnafin za su tsaya ga beraye masu ƙafa biyu da abin ya zo da sauki, amma sai su bar beraye su zo suna tayarwa talakawa hankali.
Allah ya tsare mu daga sharrin `yan kidnafin.
✍ Allemawy
Daga
MIFTAHUL ILMI
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248