SECULARISM DAGA INA ZUWA INA? [1]

SECULARISM DAGA INA ZUWA INA? [1]


_______________________
_______________________

Bayan kaurewar yakin Faraskur a shekarar 648 Ah (1250 CE) Tsakanin Musulumai da gamayyar Kiristocin Yamma karkashin jagoranci Sarkin Farance Louis IX (Na tara) a kasar Masar wanda musulmai su kaci galaba harma suka yi nasarar kama Sarki Louis din a matsayin firsinan yaki a wannan lokacin. bayan ya samu anfanshesa ya koma kasarsa ya gano cewa dole salon yakin su da musulumi ya canza daga yaki na gaba da gaba zuwa yaki na kwakwalwa ta hanyar jefawa musulmai shakku kan addinin su da yada mugayen akidu wanda akalla in basu koma kiranstanci ba to asamu su saki nasu addinin ta yadda za su samu rauni su koma yakar junansu wanda hakan shi zai bawa turawan daman malleku musulman da juyasu yadda suke su.

Duk da cewa komai ya canza nahiyar Turai sakamakon canji da ta samu daga kiristanci zuwa secularism amma bata canza adawa da kiyayyar da take yiwa musuluncin ba, hakan tasa suka cigaba da tafiya akan salo da tsari da wancan basaraken ya dora su na canza salon yaki a maimaikon da suna yakar muslumai da Cross a hannun su kowa yana gani to yanzu bari su maida shi cikin zuciyarsu, maimaikon da suna yakara musulmai da sunan addini da kare mutanensu daga shiga musulunci kai tsaye to yanzu bari a maida yakin ya koma da sunan yada Dimukradiyya da yakar ta'addanci da kare hakkin marasa rinjaye da sauran hujjoji makamantan wadanan, maimakon yakin gaba da gaba to kawai yanzu a dawo yakin wanke kwakwalwa da sauya tinani da kuma dasa musu wadanda za su yake su daga cikin su ,cikin hanyoyin da suka bi wajen kokarin raba musulmi da addininsa akwai hanyar yada wannan muguwar akidar nan ta Secularism wanda sakamakon haka da yawa daga cikin musulmi suka rungumeta suka tashi tsaye suna tallatata da kuma kareta ba dare ba na rana.

Duk sanda ake son gane hakikanin abu akan maida shi ne zuwa tushensa da asalinsa hakan shi zai sa a fahimcesa a gane inda ya samo tushe da kuma inda ya dosa. Kasancewar secularism din da yake kasashen muslmai bakwainine ba cikakke ba sai kaga mutun ya yarda a dabbakata a iya wani sashi banda wani sashi na rayuwa misali ayita a aikace a bangaren siyasa amma banda zaman takewa ko a iya bangren tattalin arziki ko a iya bangaren ilimi da bincike ko kaga mutun yana kira zuwa ga baiwa mutane yan ci da mutunta ra'ayi da sabani amma kuma gefe guda yana goyan bayan danne hakkin wasu da kama karya,ko kaga mutun yana kira zuwa ga dimukradiyya amma matsawar wannan dimukuradiyyar ta kawo wanda baya so masu birbishin addini to ayi juyin mulkima ba shi matsala, da sauran misalai makamantan haka. Bisa haka dole in anaso a fahimci asalin Secularism sai ankoma tushen inda ta fito anga yadda suka dabbakata a aikace hakane zai sa a iya fitar da hukunci cikakke.

Zan yi kokari a rubuce rubucen da za su biyo bayan yar wannan shimfida-da yardar Allah- su kasance a takaice akan :

-Secularism a kasahen Yamma:bayanin zai kasance akan ma'anar falsafar Secularism da tarihin samuwarta a can da kuma jiga-jiganta da dalilan da suka haifar da ita in da dama ya tabo abinda ta haifar a can.

-Secularism a kasashen musulmai :bayanin zai kasance akan tarihin samuwarta da wadanda suka taka rawar samar da ita da kuma dalilan da suka haifar da ita a kasashen musulmai.

-Halin da kasashen musulmi suke : bayanin zai kasance akan muhimman kasashen muslmai a takaice da halin da suke ciki da kuma yadda suka fada cikin wannan tsari na secularism.

Allah ya yi mana jagora

#Secularism
#Liberalism
#boko_akida

_#ABM_

Miftahul ilmi 

Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)