SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {02}

SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {02}


Maganar gaskiya ba bu wata cutar da ba ta da magani saboda Nassi ya tabbatar da kowacce cuta tana da magani, kuma ba bu cutar da za ace ba a warkewa daga ita, abinda za muyi imani da shi anan shi ne: Dole ne mu baiwa ALLAH cancantar sa na shi kaɗai ne mai bayar da lafiya da waraka ga wanda yaga dama kuma a lokacin da yaga dama.

Wasu da dama suna dauka ai ba a warkewa daga cutar Aljanu, saboda yadda suke ganin wasu idan ana maganin amma shiru ba labari, ko idan anyi maganin sun bar jikinsu sai can kuma aga sun sake dawowa, abin yana matukar daurewa wasu mutanen kai matuƙa.

Sai ka rasa daga ina matsalar take ne, shin Ruqyar ce mai yinta bai iya ba, ko maganin ne mai bayarwar bai san kan magungunan ba, ko dai kuma matsalar daga ita ko shi mai fama da lalurar ne?

Maganar Gaskiya dai itace: Jinnu za su iya barin jikin Mutum matuƙar ambi ka'idoji da kuma sharuddan da za su taimaka har Allah yasa hakan tafaru cikin iko da hikimar SA Mamallakin lafiya da rayuwa. Duk da kuwa akwai wasu bambance-bambancen a hanyoyin da jinnu ke samun damar shiga jikin mutane har su samu wurin zama ta yadda kuma ficewarsu sai anyi da gaske ko ma kaga sun nuna ba za su fita ba saboda sabon da sukayi da jikin da suke cikinsa ko kuma wani alqawari ne dake tsakaninsu da wanda ya turo su.

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji ci gaban lamarin...

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)