WASU MATAN // 07
Ban san yadda aurensu ya kasance ba don ba su ba da labari ba, na same su da tsufansu ne, zuwa lokacin ban taba ganin tsufa irin wannan ba, a matattararmu dai ta malam Bahaushe ba a cika ba wa soyayya mahimmanci ba, in ma za a yi din to ba a gaban yara ba, amma su kam a gaban kowa ma yin abinsu suke, ina ganin a cikinta suka tsufa, ita dai matar ba ta da wani sukuni matuqar maigidan yananan.
.
Idan ka dan waiwaya ba ka gan ta ba ba ko tantama tanacan wurinsa suna hira, ko magana za ka yi da ita in dai hirarsa za ka yi to lallai za ta yi tsayo.
.
Mu da yake yara ne mukan ji haushi wani sa'in yadda takan nuna damuwarta sosai a kan yadan yi qari bisa lokacin da ya saba dawowa, dan kuci-kuci kadan "Alhaji ko lafiya oho! Na ga shuru har yanzu" wani sa'in mukan tambayi kammu ko so take a nemo mata shi?
.
Bayan mun mallaki hankalinmu muka fara fahimtar irin shaquwar dake tsakaninsu har muke cewa: Anya in wani ya kwanta dama dayan ba zai bi shi ba kuwa? Don abin a ganimmu ya yi yawa gaskiya, ko a fima-fiman yanzu sai haka.
.
Ai kuwa 'yan watannin baya kadan sai Maiduka ya amshi ran matar, duk mun ji rasuwar a jikinmu amma muna jin tsoro abin da zai iya abkuwa, wallahi ina ganin kiran abokaina biyu na ce "Alhaji sa'i ya yi" ilai kuwa, shi ma din ya bi ta, irin wadannan matan kamar haka masamman Allah SW yake halittarsu, Allah ya yi musu rahama gaba daya.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248