SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {03}


SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ? {03}

A rubutun da ya gabata na BAMBANCI munyi bayanin wasu abubuwan da suke yin sanadiyyar shigar jinnu jikin mutum saboda sakacin yin Azkaar da rashin kiyaye wasu abubuwan ko kuma afkawa cikin wasu abubuwan da suke da abota da shaidanu ta hanyar yiwa wani Sihiri ko makamantan haka, da kuma yadda za mu kiyaye wasu abubuwan domin ALLAH ya kare mana lafiyar munda kariyar sa.

Tun da mun fahimci abubuwan da suke sanya jinnu shiga jikin mutane kuma ya kamata mu fahimci abubuwan da suke dauwamar da jinnu a jikin mutum, ta yadda za su samu wurin zama har su saba da jikin mutum ficewarsu kuma ta zama babban aiki duk da maganin da ake yi kuwa.

Daga cikin abubuwan da suke sabbaba Jinnu dauwama a jikin mutumin da yake fama da lalurar shafar aljanu har Jinnun ya saba ko su saba da jikinsa su ne kamar haka:

1- Rashin karanta Alqur'ani da sauraron Alqur'ani akai akai, saboda shi Alqur'ani shi ne babban ambaton ALLAH mai girma, kuma duk wanda ya daina ambaton Allah sai ALLAH yasanya SHAIDAN yazama abokin sa na dindindin.

2- Rashin tabbatar da cewa: Lafiya da waraka duk suna a hannun Allah shi kaɗai, sai kaga ana yin imani da wasu bokaye ko wasu matsafa can dabam, har ana cewa suna iya bayar da lafiya ko suna iya bayar da warakar, tayadda kuma hakan yana cikin abubuwan da suke kara tabbatar da Jinnu a jikin mara lafiyar da ake kai shi wajan irin mutanen nan, saboda su Jinnun ko shaidanun wasa da kwakwalen mara lafiyar da ma masu yin jinyarsa kawai za su yi ta yi har lokacin da ALLAH yaso.

3- Yin maganin Jinnu da abubuwan da suka haramta a Shari'ar Musulunci, kamar: Yanka wata dabba don sadaukar da jinin ga wani aljani, yin yanka ba tare da ambatar sunan Allah ba sai dai sunan wasu shaidanun mutane ko Aljanu, ko a binne wata dabba da ranta da dai makamatansu.

Za muji ci gaban a rubutu nagaba Insha ALLAHu 

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com
Post a Comment (0)