ZA MU IYA CIN NAMAN SANIYAR DA TAKE SHAN Giya?

ZA MU IYA CIN NAMAN SANIYAR DA TAKE SHAN GIYA !


Tambaya
Assalamu alaikum, me ye hukuncin cin naman dabbar da ake shayar da ita giya ?, alhali mutane ba su san ana yanka musu irin wannan dabbar ba? 
A wani video na ga ni, makiyayin ya ce ita giyar tana sa su cin abinci sosai. ya Allah Ya sa mu dace.

Amsa
Wa alaikumus salam
Annabi SAW Ya bayyana haramcin sayar da giya a hadisin Jabir Dan Abdullahi shekarar da aka bude Makka, kamar yadda ya zo a manyan kundayan Musulunci, manyansu da kananansu.

Duka malaman Mazhabobi guda hudu sun tafi akan cewa giya najasa ce, saboda Allah Ya kirata da kazanta a cikin suratul Ma'ida, Kuma Annabi SAW ya yi umarni da kwararar da ita lokacin da aka saukar da haramcinta daga sama, kamar yadda Malik ya rawaito a Muwadda, hadisi mai lamba ta (3133).

Duk dabbar da take rayuwa akan najasa ba a cin namanta har sai an killace ta, najasar ta bi jikinta, namanta kuma ya dad'ad'a (استحالة), saboda manzon rahma ya haramta cin dabbar da take cin najasa, kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta (1824) da Abu dawud (3787).

Duk da cewa siyan giya a bawa dabba haramun ne saboda hadisin Jabir da ya gabata, sai dai in an siya an ba ta ya halatta a ci namanta mutukar ba ta sha da yawa ba, ta yadda za ta zama ita ce mafi rinjayan abincinta, kamar yadda malaman fiqhu suka yi bayani.

A bisa abin da ya gabata ya halatta a ci naman wadannan Shanu tun da giyar kadan ce ake gauraya musu a ruwa, saboda abin da yake d'an kadan bai cika tasiri ba, Kuma zai iya sajewa da abin da ya gauraya da shi, Dalilan Sharia sun tabbatar da afuwa akan najasa 'yar Kadan.
العين المنغمرة في غيرها هل هي كالمعدومة أم لا ؟

Ya wajaba masu kiwo su ji tsoran Allah su daina ciyar da dabbobinsu da Haram, da abin da zai iya cutar da mutane in sun ci.

Algus a cinikayya yana debe albarkar kasuwanci, ya zo a hadisin da Muslim ya rawaito "Duk Wanda ya yi algus ba ya cikinmu"

Duba littafin Ibnu Rajab:
تقرير القواعد وتحرير الفوائد. 

Allah Ne Mafi Sani 
Dr. Jamilu Zarewa
6/1/2023
Post a Comment (0)