ALHERI SHI NE KOYON FIQHUN HADISAN ANNABI (SAW)

ALHERI SHI NE KOYON FIQHUN HADISAN ANNABI (SAW)


Shaihukul Islami (r) ya ce:
الخير كل الخير في اتباع السلف الصالح والاستكثار من معرفة حديث رسول الله صلى الله عليه وسلم والتفقه فيه والاعتصام بحبل الله وملازمة ما يدعو إلى الجماعة والألفة ومجانبة ما يدعو إلى الخلاف والفرقة؛ إلا أن يكون أمرا بينا قد أمر الله ورسوله فيه بأمر من المجانبة فعلى الرأس والعين. وأما إذا اشتبه الأمر هل هذا القول أو الفعل مما يعاقب صاحبه عليه أو ما لا يعاقب؟ فالواجب ترك العقوبة؛ لقول النبي صلى الله عليه وسلم {ادرءوا الحدود بالشبهات فإنك إن تخطئ في العفو خير من أن تخطئ في العقوبة} رواه أبو داود ولا سيما إذا آل الأمر إلى شر طويل وافتراق أهل السنة والجماعة؛ فإن الفساد الناشئ في هذه الفرقة أضعاف الشر الناشئ من خطأ نفر قليل في مسألة فرعية.
مجموع الفتاوى (6/ 505)

"Dukkan alheri yana cikin Bin tafarkin Magabatan kwarai (Salaf) da YAWAITA NEMAN SANIN HADISIN MANZON ALLAH (SAW) DA NEMAN SANIN FIQHUNSA, DA RIKO DA IGIYAR ALLAH DA LAZIMTAR DUKKAN ABIN DA YAKE KAIWA GA JAMA'A DA HADIN KAI, DA NISANTAR DUKKAN ABIN DA ZAI KAI GA SABANI DA RARRABUWA, sai dai in ya kasance abu ne bayyananne da Allah da Manzonsa suka yi umurni da nisantarsa (kamar hadin kai a kan bata da Bidi'a ko Uquba wa 'yan bidi'a ta hanyar kaurace musu) to wannan kam mun ji kuma mun bi.
Amma idan lamari ya rikice aka kasa gane matsayin ra'ayi ko aiki shin za a yi Uquba wa ma'abocinsa ko a'a?
Abin da yake wajibi shi ne barin Uqubar....
Musamman idan hakan zai haifar da sharri mai tsawo da rarrabuwar kan Ahlus Sunnati wal Jama'a, saboda barnar da take cikin rarrabuwar ta ninninka sharrin da yake faruwa daga mutane 'yan kadan a kan karamar mas'alar Addini".

ABIN LURA:
(1) Dukkan alheri ya tattara cikin wadannan abubuwa:

1- Riko da Igiyar Allah; Qur'ani da Sunna.
2- Neman Ilimin Hadisan Annabi (saw) da sanin Fiqhunsu.
3- Bin tafarkin Salaf.
4- Riko da dukkan abin da zai janyo hadin kai a kan Igiyar Allah da hadin kan Ahlus Sunna.
5- Nisantar dukkan abin da zai kai ga rarrabuwar Ahlus Sunna da sabani a tsakaninsu.
6- Yin Uquba na kauracewa ko Tahziri ko makamancinsu a kan kananan mas'alolin Addini raba kan Ahlus Sunna ne da tayar da fitina.

(2) A cikin wannan akwai fifita Maslahar hadin kai da Barnar rarrabuwa a kan barnar masu kuskure.

# _Dr. Aliyu Muh'd Sani_
    
Miftahul ilmi 
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://chat.whatsapp.com/ILkMqIQo7IZDrMREp92R01
Post a Comment (0)