TSAKANIN SO DA SOYAYYA // 07
To in za mu lura da ma'anar soyayya wace a kowani lokaci take nufin qaunar juna daga rayuwa har mutuwa, gami da buqatuwar yalwatuwar zuriyar da Annabi SAW zai yi alfahari da ita ranar qiyama, da sadaukar da kai don gabatar da kowace iriyar hidima wace dai ba ta saba wa Allah SW ba, za mu ga mai yin ta ba zai iya murtsike idanunsa ya je wajen uban yarinya ko da arne ne ya ce masa " Ina qaunar yarinyarka kamar na mutu, amma qaunar ta sa'o'i hudu ce ko biyar, ko shekara shida ko bakwai, ko ya ce masa wallahi ina son ta so na haqiqa amma ban son ta haihu da ni, ko ya ce "Zan aure ta na wani lokaci, kuma zan ba ta duk abin da take so amma matsayinta ba kamar sauran matana ne da nake raba musu ci da ciyarwa ba, don haka danta ba zai yi gaje na ba, kamar dai yadda mutu'a take, ko kuma na ce zina wato sunan da kowa ya fi saninta da shi.
In fa ka dunfari wani uba da wannan maganar ba wai wautarka kadai zai gani ba, sai dai Allah ya raba ku, to duk wasu irin kalmomi masu tsada, wadan da suke tafiya da imanin uwar mata ma ba wai budurwa ba, samarin yanzu 'yan bana bakwai suna amfani da su ne wajen yin zance da 'ya'yammu, abin haushi ma mun bar jaki mun koma dukan taiki, (Kamar ya?) Yauwa, in da za ka lura ka kira matarka da suna "Matar kulle" ka hana ta zama da duk wani da namiji duk da cewa babbace mai hankali ba qarama bankaura ba, ka ce kar a shiga maka gida, tare da sanin mazinatan yanzu in gida da yara ga sauran jama'a ba za su iya fado maka gida da rana tsaka ba,
To 'yar qaramar yarinya mai guntun tunani wace ba ta san waye namiji ba za kabar ta ta kebance da shi cikin dare cinya na gugar cinya da sunan soyayya? Ko kana tunanin ta fi uwarta iya tsare kanta ne? Na san dai da wahala ka ce ai uwar taka ce shi ya sa ka tsare ta, 'yar kuma ta wani ce to ya je sai yadda ya yi da ita, haba dai! Ai ba kowane so ne soyayya ba, ko da kuwa an kira shi da hakan, duk lokacin da aka bata wa mutum 'ya ita da miji sai dai wani ya aure ta don kudin uban, ko kyawunta, to amma ba don addininta ba, don kuwa namijin da aka yi kuskuren ba shi aminci ya gama da ita, har ma da iyayenta gaba daya.
Bari ka ga yadda ake zaben abokin rayuwa: Hafsah 'yar Umar RA bazawara ce ba ma budurwa qarama ba, amma mahaifinta bai yi sakaci ya bar ta a gida da hujjar cewa ta mallaki hankalinta sai ta kawo mijinta da kanta ba, sai ya duba kamilin mutum, wanda hatta Annabi SAW ya shede shi wajen kamala da kunya wato Usman RA, ya tallata masa ita, bai yi qasa a gwiwa ba don bai amsa ba, ya miqa wa Abubukar RA, na hannun damar Annabi SAW, ba shakka wannan Zabi ne mai tsada, wanda uba na gari yake qoqarin yi wa diyarsa, wace ko alama ba za ta ce ana qoqarin yi mata auren dole ba, wato an qi bari ta zabo wanda ita ce za ta zauna da shi ba iyayenta ba, alhamdu lillah, da haka ne Allah SW ya dubi qirazansu ya aurar da ita ga fiyayyen halittu, wato Annabi SAW, wanda dalilinsa din ne Usman RA da Abubakar RA suka ka ja da baya.
Ta irin wannan hanyar ce dai, Annabi ya zabo Usman RA ya aura masa Ruqaiyya RA, da ta rasu ya qara masa da Umm Kulsum, har ma ya ce in da yana da wata da ya qara masa, amma ba wata daga cikinsu da raina zabin uban ta ce a bar ta ta zabo mijinta da kanta, haka dai Annabi SAW ya aura wa Fatima RA Aliy RA, mu a ruwayoyimmu na sunna ta riqe shi hannu bibbiyu ba ta qi shi ba ta yi wa mahaifinta tsayayya ba.
Wato soyayya kuwa ta gani ta fade, sai ta Zainab RA babbar diyar ma'aiki da ta auri Abu As bi Amir, an aika ta dawo gida don muslunci ya saukar da hana zaman musulma a qarqashin arne, amma da aka kama shi a matsayin fursunan yaqi, ta dauki sarqarta wace ta gada daga nahaifiyarta Khadija ta tura wa qanin mijinta ta ce ya fanso shi ita, a wani sumame da aka kai musu kuma ta nema masa mafaka, amma ba ta saba wa mahaifinta ba duk da bala'in son da take wa mijinta, haka ta zauna a gida har sai da ya muslunta ta koma masa, duk magabatan nan sun gina soyayyarsu bayan aure ne amma komai na su iyayensu suke shirya shi.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248