WASU MATAN // 11
Wasu matan sun fi maza tunani sosai da gaske, amma tsakani da Allah tunaninsu kadan ne, don ba sa tuna baya, kuma ba su damu da abinda zai faru gaba ba, sun riga sun yi abinda za su iya komai tafanjama-fanjam, in tunani ya zama irin wannan to gaskiya qwaqwalwa ba ta da amfani.
.
Wannan bazawara ce ma ta auri wani dan mataliki da 'ya'yansa da dama, koda yake Allah cikin ikonsa 'ya'yan mata ne, kuma duk sun yi aure kowa tana gidan mijinta, sai dai duk da haka akwai qawazuci irin na mahaifa, suna matuqar son mahaifinsu wata ta janye shi.
.
Wannan matar tunda ta shigo gidan ta ratsa tsakaninsu da mahaifinsu, ya dena hira da su kamar yadda ya saba, in ma magana zai yi da su na dan qaramin lokaci ne, har dai yaran suka gano abinda yake faruwa, ko kyauta zai yi musu sai dai a boye, galibi ma ita take yanke abinda za a ba su, wani sa'in in ya ba su ta ce ya yi yawa a rage.
.
Sai da aka kai ba sa iya kwana a gidan in wani sha'ani ya kawo su garin, abinci ma sun gwammace su ci a wurin maqwabta qawaye da 'yan uwa.
.
Babban abinda yake damunsu uban nasu ba ya jin dadin abinda yake yi, amma ba zai iya canjawa ba, ya bayyana qarara tsoronta yake ji, ta shigo gidan ta lalata komai, don ba 'ya'yansa ba har 'yan uwansa ba sa son zuwa wurinsa, ita ma ba ta qaunar ziyartar kowa, ta maida shi marowaci na qarshe.
.
Wanda kowa yake jin tsoronsa in ya yi magana kamar sarar wuqa sai gashi yana nisantar mutane, ya kwashe tsawon lokaci bai ziyarci kowa ba, in kuma an ziyarce shin sai abinda matarsa ta ce, ba wanda ya isa kuma ya yi maganarta a gabansa, in ma kana son ku bata to ka dauko maganarta, yana da dan wurin sana'a in yaran suka yi amfani da shi komai kasawarsa sai sun biya, sai dai in matarsa ba ta ga lokacin ba, me ya sa irin wadannan matan suke haka?
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248