TUBA BAI TAKAITA A KAN AIYUKAN ALFASHA DA SABO KAWAI BA

TUBA BAI TAKAITA A KAN AIYUKAN ALFASHA DA SABO KAWAI BA


Zunubai da Allah ya wajabta tuba daga garesu ba su takaita a kan zunuban da bawa ya samesu ta hanyar aikata sabo da alfasha kawai ba, a'a, sun hada har da zunubai da bawa yake samu ta hanyar barin aikata wasu aiyukan da'a wajibai. Saboda da'a ma Allah ya hada aikata aiyukan da ya yi umurni da aikatawa, da kuma nisantar aiyukan da ya yi hani. Idan bawa ya bar aikata aiyukan da'a wajibai to zai samu zunubi, kuma imanin da ake so ya cika a bisa wajibi (Imani na wajabi) ya ragu. Haka idan ya aikata aiyukan haramun da kaba'irai to zai samu zunubi, kuma imanin da ake so ya cika na wajabi ya ragu. Saboda haka, kamar yadda muke neman tuba a wajen Allah a kan aiyukanmu na sabo da alfasha, haka ya wajaba muna tuba daga zunubanmu da muka samu a sakamakon barin wajibai na aiyukan da'a ma Allah, kai hasali ma tuba daga barin wajibai shi ya fi girma kuma ya fi amfani ma bawa.

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
وكثير من الناس لا يستحضر عند التوبة إلا بعض المتصفات بالفاحشة أو مقدماتها أو بعض الظلم باللسان أو اليد وقد يكون ما تركه من المأمور الذي يجب لله عليه في باطنه وظاهره من شعب الإيمان وحقائقه أعظم ضررا عليه مما فعله من بعض الفواحش فإن ما أمر الله به من حقائق الإيمان التي بها يصير العبد من المؤمنين حقا أعظم نفعا من نفع ترك بعض الذنوب الظاهرة كحب الله ورسوله؛ فإن هذا أعظم الحسنات الفعلية
مجموع الفتاوى (10/ 329)

"Da yawa daga cikin mutane a lokacin tuba, ba sa kawo wasu laifuka a tunaninsu sai zunubansu na Alfasha, ko magabatan Alfasha (aiyuka da suke kasancewa kafin aikata zina da makamancinta), ko wani daga cikin zaluncin da suka aikata da baki ko da hanu, alhali kuma ta yiwu abin da mutum ya bari na aiyukan da aka umurce shi da ya aikata, wadanda suka wajaba a kansa na da'a ma Allah na boye da na bayyane da suke cikin Rassan Imani da hakikaninsa (tushensa da manyan wajibansa) ta yiwu sun fi girman cutarwa a gare shi fiye da abin da ya aikata na Alfasha. Saboda abin da Allah ya yi umurni da shi na hakikanin Imani wadanda da su bawa yake zama cikakken mumini ta yiwu sun fi zama masu amfani fiye da amfanin barin aikata wasu aiyukan zunubai bayyanannu (aiyukan sabo), misali SON ALLAH DA MANZONSA (SAW), lallai wannan shi ne mafi girman kyawawan aiyuka da ake so a aikata".

Abin lura:
1- Imani da Taqwa (jin tsoron Allah) shi ne aikata aiyukan da Allah ya yi umurni, da nisantar aiyukan da ya yi hani.
2- Allah ya fi son ka aikata abin da ya umurceka da ka aikata na wajibi fiye da nisantar abin da ya haramta.
3- Allah ya wajabta mana tuba daga dukkan zunubai.
4- Kamar yadda muke mai da hankali wajen tuba daga aiyukan haramun da sabo, to ya kamata mu fi mai da hankali a kan tuba daga zunuban da muke samu a sakamakon sakaci da barin aikata wajibai.
5- Allah ya wajabta mana aiyuka masu yawa, wadanda dukkansu suna cikin rassan Imani na wajibi, kuma akwai da yawa daga cikinsu da suke bangaren kyawawan halaye da dabi'u, amma sai ka samu kadan ne daga cikin mutane masu aikatasu, kuma mutane ba sa damuwa, bare har su tuba a kan barinsu da suka yi.
6- Akwai manyan aiyuka wadanda su ne hakikanin Imani da tushensa, wadanda suke aiyuka ne boyayyu a zuciya, kamar Son Allah da Manzonsa, da gaskata Allah, da samun yaqini a kan Allah da Addininsa da lamura na Imani, kamar Imani da Gaibi, abubuwan da suke bukatar mutane suna rayasu suna aikatasu a cikin zukatansu har su kai matsayin kamala a imani na boye har ya kaisu ga kamala a Imanin na bayyane.

 Dr. Aliyu Muh'd Sani
      Feb 02, 2015



Miftahul ilmi 
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://chat.whatsapp.com/ILkMqIQo7IZDrMREp92R01
Post a Comment (0)