AƘIDUN SHI'A DA TA'ADDANCINSU A TSAWON TARIHI //01
WALLAFAR: Malam Najeeb El-Kabir Kwarbai
MA'ANAR SHI'A: Kalmar Shi'a tana ɗaukar ma'anoni guda biyu, ma'ana ta farko a harshen larabci, ta biyu kuma isɗilahin shari'a (ma'anarta ta shari'a)
MA'ANARTA A HARSHEN LARABCI: Ana ƙiran kalmar “Shi'a” a harshen larabci da ma'anar mabiya (At-ba'u) da kuma mataimaka (Ansaru).
MA'ANARTA A ISƊILAHI NA SHARI'A: Malamai da yawa sun bada ma'anar Shi'a da ma'anoni daban-daban, waɗanda a ƙarshen ma'anonin suna komawa ne zuwa ga abu ɗaya.
Idan muka koma littafan Shi'a kuma, za mu ga cewa ma'anar na komawa ne ga abu ɗaya shima. Shi ne tabbatar da cewa Abubakar (RA) da Umar (RA) dukkansu basu cancanci jagoranci da shugabancin da suka yi ba a bayan Manzon Allah (SAW) ba, kuma mulkin da suka yi ƙwace ne. Saboda haka ne suka halasta la'antarsu da zaginsu, kamar yadda ya zo a cikin littafinsu mai suna “Ihƙaƙul Haƙ 1/337” da littafin “Biharul Anwar 29/137” inda suka ƙira Abubakar (RA) da Umar (RA) da sunan Gumaka kuma Kafirai (Wa'iyazu billah).
WASU DAGA CIKIN MA'ANONIN DA MALAMAI SUKA BAYAR GAME DA MA'ANAR SHI'A.
● Ibnu Athir Yana cewa: “Wannan suna na Shi'a ya rinjaya (shahara) ne a kan duk wanda yake cewa yana son Aliyu (RA) da Ahalinsa (Iyalan gidansa), har sai hakan ya zama wani suna ne garesu. Idan aka ce: “Wane ɗan Shi'a ne”, to an san cewa yana cikin su ne. Ko a littafan fiƙhu ko Aƙida a ce: A Mazhabin Shi'a kaza ne, to ana nufin a wajen su.” [Duba: Lisanul Arab: 8/188, Bugun Maɗaba'ar Darul Sadri a Beruit, bugu na 1. Shekarar 1410 bayan hijira-1987 Miladiyya]
● Abu Musa Al-As'ariy Yana cewa: “Kawai an ƙira su da suna Shi'a ne, saboda sun ɓangaranci Aliyu (RA), kuma suna gabatar da shi akan sauran Sahabban Manzo Allah (SAW).” [Duba: Almuqalatul Islamiyyin 1/65, Tahqiqin Muhammad Muhyid-deen Abdulhamid Badun].
● Ibnu Hazmin Yana cewa: “Duk wanda ya dace da Shi'a (ma'ana yayi daidai dasu wajen cewa Aliyu (RA) shi ne yafi dukkan mutane (Sahabbai), kuma shi ne yafi cancanta da imamanci, da shi da ƴaƴanshi a bayanshi, to ɗan Shi'a ne. Ko da ya saɓa musu a abubuwan da ba wannan ba. Idan ya kuma ya saɓa musu abubuwan da muka ambato, to ba ɗan shi'a ba ne.” [Duba: Al-Fisal Fil Milal Wan nihal 2/113, Bugun Maktabar Al-khaniji a Misra].
● Imamu Shaharastany Yana cewa: “Shi'a su ne waɗanda suka ɓangarantu da Aliyu (RA) a keɓance, kuma suka ce shi ne Imami, kuma shi ne Halifan Manzon Allah (SAW) a nassance (Alƙur'ani da Hadisi) da wasiyyance, ko a baytane ko a ɓoye. Kuma suka ƙudurce cewa Imamanci ba zai fita daga ƴaƴansa ba. Idan har ya fita, to zalunci be daga waninsu.......” [Duba: Al-Milal Wal Nihal 146, Tahqiqin Abdul'aziz Muhammad Alwakil. Bugun Darul-fikr Beruit, Lebanon].
Zamu ci gaba in shaa ALLAH.