AƘIDUN SHI'A DA TA'ADDANCINSU A TSAWON TARIHI //02
WALLAFAR: Malam Najeeb El-Kabir Kwarbai
WASU DAGA CIKIN MA'ANONIN SHI'A A ISƊILAHI DA MALAMAN SHI'A SUKA BAYAR.
● Muhammad Al-Hussain Aali Kashif Algiɗan Yana cewa: “Lallai adadin waɗanda suka keɓantu da Aliyu (RA) kuma suka lazumce shi a zamanin Manzon Allah (SAW) ba kaɗan ba ne, kuma suka sanya shi a matsayin Imami, mai isarwa ga mutane daga Manzon Allah (SAW), kuma mai sharhi da bayani a kan abubuwan da ya koyar. Kuma shi ne sirrorin hukuncinsa da hukunce-hukuncen da ya yanke, haka ya sanya suka zama mabiya ga Aliyu (RA), kamar wata alama da ta keɓanta da su kawai. Kamar yadda masana harshen larabci suka faɗa.” [Duba: Aslu Shi'a wa Usuliha 45, bugun Mu'assasatu Al-A'lami Beirut]
● Abu Muhammad An-Naubakhtiy Yana cewa: “Su ne jama'ar Aliyu Bin Abi Ɗalib (AS), waɗanda ake ƙiransu da suna Ƴan Shi'an Aliyu (RA) a lokacin Annabi (SAW) da kuma bayan rayuwar shi. An san su ne ta hanyar komawa zuwa gare shi, da kuma magana akan Imamarshi da suke yi. Waɗannan mutane kuwa sune; Miqdad Bin Aswad da Salman Al-Farisi da Abu-Zarr Jundubi Bin Junadah Algifary da kuma Ammar Bin Yasir da duk wanda soyayyar shi ta dace ga soyayyar Aliyu (RA). Su ne farkon waɗanda aka sanya musu suna Shi'a a cikin wannan al'ummar. Saboda sunan Shi'a, wani abu ne sananne tuntunin, kamar Shi'ar Ibrahim da Musa da Isah da sauran Annabawa Amincin Allah ya tabbata a garesu baki ɗayansu.” [Duba: Firaqu Shi'a 28-29, bugun Darul Rashad, tahqiqin Dr Abdulmuna'im Alhafniy, bugu na 1. Shekara ta 1412-1992]
Idan muka tattara dukka waɗancan ma'anoni da aka kawo daga ɓangaren Shi'a, za a ga cewa duka suna komawa ne zuwa ga abu ɗaya, wato tabbatar da Imamanci ga Aliyu (RA) da kuma barranta ga sauran Sahabbai, sai ƴan kaɗan.
ASALIN SHI'A: Bincike mai zurfi na masu bincike, da bin diƙin-diƙin na masana tarihi sun tabbatar da cewa asalin Shi'anci ya samo asali ne daga wani bayahude, wanda ya shigo cikin adfinin Musulunci domin ɓata addinin. Wannan mutumin sunan shi Abdullahi ɗan Saba'i, kuma shi ne ya ƙirƙiro Shi'a masu cewa: “Aliyu (RA) Allah ne!” (wa'iyazu billah) kuma mutumin shi ne ya kawo tunanin (Fikrar) cewa Aliyu (RA) shi ne wasiyyin Manzon Allah (SAW) kamar yadda Yusha'u ɗan Nuh ya kasance wasiyyi ga Annabi Musa (AS), hakanan kuma dukka Annabawa su guda dubu ne, kuma kowannensu yana da wasiyyinshi. [Duba: Tarikhu Ɗabariy 2/378-379, bugun Al-Istiƙama, Al-ƙahira]
Haka nan Abdullahi ɗan Saba'i shi ne ya ƙirƙiro musu aƙidar raja'a (Bayani zai zo akan shi nan gaba) da kuma aƙidar tawaye ga shuwagabanni.
Malamai masu yawa daga ɓangaren Sunnah da ɓangaren Shi'a, har da ɓangaren waɗanda basa amsa sunan Musulunci, sun tabbatar da a tarihi an yi wannan bawan Allah.
Zamu ci gaba in shaa ALLAH.