DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [3]

DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [3] 



Akwai dalilai masu yawa da suka taimaka wajen yaɗuwar tafarkin Rafilanci a nan ƙasar. Za mu duba muhimmai daga cikinsu. 

Dalili Na Farko:  Gazawar Malamai 

Dalili na ɗaya kuma mafi muhimmanci, shi ne gazawar malamai a shugabancin jama’a da shiryar da su, da yi musu jagora da katangance su daga ɓata. Domin famintar wannan dalili za mu kasa malamai gida uku [kashi na farko da na biyu sun gabata]

Saboda rashin kalmar da ta fi, za mu kira kashi na uku na malaman da sunan BURAZOZI wanda wannan hausancewa ne na kalmar “brothers” ta Turanci wace take nufin ƴan uwa. Abinda nake nufi da burazozi, ko kuma ƴan Buraza kamar yadda aka fi sanin su, su ne mutane, yawanci matasa, waɗanda suke da son Musulunci a zuci amma kuma galibi suke da ƙarancin saninsa. Yawanci suna sanin Musulunci ta hanyar sauraron laccoci a wurin taruka, karanta ƙasidu da maƙalu a cikin jaridu na yau da kullum da kuma mujallu masu kulawa da al’amuran Musulmi. Yawancinsu ɗalibai ne masu karatun fannoni dabam-daban a manyan makarantu da jami’o’i kamar fannonin kimiya, fasaha, tattalin arziki, likita, lauya da sauransu.  Kaɗan ne daga cikinsu suka karanta Musulunci kuma a mataki na ƙasa ainun, imma I.R.K. a makarantun sakandare ko kuma ƙaramar faifa ta aro a jami’a. 

Kamar yadda na faɗi a baya, yawancin waɗannan matasa ne masu tsananin son addini da kishin sa amma kuma babu wadatar ilminsa. Idan ka haɗa ƙarancin sani da tsananin kishi da gafin ƙuruciya, sai ka samu wani kwaɗo mai haɗari. Kuma da yake yawanci suna jin Turanci, harshen da shi ne ake yin amfani, kuma ake burga, da shi a makarantu, wannan sai ya ba su damar shaƙe wuyan makirfon da faɗi a saurare su, koda abinda za su faɗi ɗin ba shi da nauyi ainun. Wani babban abinda yake ƙara tauye su shi ne rashin jin Larabci kuma kamar yadda aka sani duk wanda bai jin Larabci to ba ya shan kunun Musulunci sai dai ya sha farau – farau.  Wannan kashi na “malamai” daga cikinsu ne yawancin ƴan Shi’a suka fito, ciki har da madugunsu Malam Zakzaki.

Wannan bayani duka ba yana nufin cewa wannan kashi na malamai bai yi wa Musulunci kome ba; a’a. A haƙiƙa ƴan Buraza sun toshe wata babbar kafa a makarantunmu wacce, musamman a shekarun 1970 da 1980, ba mai iya toshe ta sai su.  Sun taimaka ainun wajen tsayar da ibadoji, kamar sallah da azumi, a makarantu, sun tari ƙalubalen ƙungiyoyin Kirista kuma sun taimaka wajen yaƙar malamai da ɗalibai masu karkata ga tafarkin Gurguzu a jami’o’inmu a lokacin da Kwaminisanci yake yaƙar addinai da al’adu a ƙasashe masu tasowa. 

Sai dai wannan kashi na malamai, da yawa daga cikinsu, bayan sun manyanta kuma sun taka matakin shugabanci da tasiri a cikin al’umma, har yau abin takaici suna nan suna yaɗa Shi’a, wasu a kan rashin sani wasu kuma a bisa ganganci. Daga cikinsu, ga misali, akwai wani ɗan jarida mai ƙima a idanun makaranta, wanda ya yi rubutu a wata jarida wacce ake mata kallon ta Musulmi ce, yana cewa wai ƙiyayyar da Larabawa suke nuna wa mutanen Iran ƙiyayya ce da aka gina ta a kan ƙabilanci, yana nufin saboda su ƴan Iran Farisawa ne ba Larabawa ba, kuma wai saɓanin dake tskaninsu ba na aƙida ba ne. Babu shakka wannan ɗan jaridar imma dai ya shiga fagen da ba shi da sani a kai, abinda bai dace da ɗan jarida mai mutunci da amana ba, ko kuma yana yaudarar makarantansa ne da gangan. [Domin tabbatar da haka, duba littafinmu Matsayin Musulmi a wajen ƴan Shi’a].

Akwai wani Farfesan Tarihi (amma ba Tarihin Musulunci ba) wanda ya ba da lacca a munasabar bikin Ashura na ƴan Shi’a na shekarar 1432/2011 a Kano, inda ya ce wai ranar da Hussaini (RA) ya yi shahada ita ce rana mafi muhimmanci a tarihin Musulunci. 

Abin mamaki! Ba ranar da Annabi(SAW) ya yi hijira zuwa Madina ba (wacce Sahabbai suka zaɓe ta, don muhimmancinta, ta zama rana ta farko a kalandar Musulunci); ba ranar yaƙin Badar ba (wacce Allah ya kira ta a cikin Alƙur’ani: Yaumal Furƙani: Ranar rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya); ba ranar Sulhun Hudaibiyya ba (sulhun da Allah ya kira shi a cikin Alƙur’ani: Fatahan Mubina: Buɗi mabayyani); ba ranar Fatahu Makkata ba (ranar da aka kawo ƙarshen bautar gumaka a ƙasar Larabawa); a’a, ranar da Hussaini ya yi shahada ita ce mafi muhimmanci a tarihin Musulunci! Ban sani ba wannan jahilci ne daga ɓangaren Farfesan ko kuwa ya sha farfesun Iran ne, shi ya sa yake faɗin haka da gan-gan don ya ɓatar da mutane? 

Kuma wasu jaridu da ake wa kallon cewa su na Musulmi ne sun ɗauko wannan bankaura ta Farfesan, sun buga ta, suna yaɗa ta a tsakanin al’umma. Shin rashin sani ne wannan ko kuwa wata ƙullalliya ce? Ta yaya ƴan jaridarmu za su jahilci addininmu? Ko ta ƙaƙa mutanen da aikinsu ne ilmantar da jama’a da faɗakar da su da wayar da su, za su komo suna yi musu rufa-ido? 

Na karanta wata maƙala a cikin jaridar Daily Trust fitowar Alhamis, 23 ga watan Fabrairu, 2012 shafi na 52, inda wata ma’aikaciyar jaridar mai suna Hajiya Wance ta ruwaito wani malamin Shi’a yana zargin Sayyidina Abubakar da Sayyidina Umar, Allah ya ƙara musu yarda, da cewa wai sun yi mubaya’a ga Ali binu Abi Ɗalib (RA) a kan khilafa a gaban Annabi (SAW) amma bayan rasuwar Annabi ɗin sai suka warware wannan mubaya’ar. 
Sai na yi mamaki yadda jaridar za ta tallata wannan zargi na Shi’a tare da cewa zargin ya saɓa da tarihi ingantacce, kuma tare da cewa zargin yana tattare da ɓatanci ga waɗannan manyan Sahabbai. Na ce a raina da wani ɗan Majalisar Dattijai ne ko Majalisar Wakilai aka yi wa wannan zargi da wata ƙila jaridar sai ta tuntuɓe shi, ko ta tuntuɓi wani mataimakinsa, kafin ta buga zargin don ya kare kansa ko ya ƙaryata, kamar yadda jaridu masu mutunci suke yi. (Wani da ba na tuhuma da ƙarya ya tabbatar mun da cewa sun aike da martani daga baya, amma jaridar ba ta buga ba). 
Ita wannan musakar Hajiyar da ta rubuta maƙalar da Editanta jahili, ko munafuki, da ya buga ta ba su sani ba cewa warware mubaya’a babban laifi ne a Musulunci wanda bai kamata a dangana shi ga gama-garin Musulmi ba, balle Sahabi, balle shugabannin Sahabbai irin su Abubakar da Umar, musamman kuma da yake wannan mubaya’ar an yi ta da umarnin Annabi (SAW) kuma a gabansa. Dangana musu wannan laifi zargin su ne da aikata FASIƘANCI. 

 Imam Muslim ya fitar da hadisi daga Abu Sa’id Alkhuduri (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan aka yi mubaya’a ga khalifofi biyu to ku kashe na baya daga cikinsu.” [Sahih Muslim]. Da yake sharhin hadisin, Imam Nawawi ya ce, “Ma’anar hadisin: Idan aka yi mubaya’a ga wani khalifa bayan an riga an yi ga wani, to mubaya’ar na farko ita ce ingantacciya kuma wajibi ne a cika ta. Sa’an nan mubaya’ar na biyun ɓatacciya ce kuma haramun ne a cika ta. Haka nan haram ne gare shi (khalifan na biyu) ya neme ta (mubaya’ar tasa).” [Duba Sharhu Sahih Muslim na Imam Muhyiddin binu Sharaf Annawawi, bugun Darul Fikir, Bairut, 1401, mujalladi na 12 shafi na 231].

  Mai karatu yana iya gani a fili cewa waɗannan talukai biyu, ina nufin Hajiya musaka da jahilin Edita, sun taimaka wajen tallata wannan zargi na ƙarya kuma sun dangana wa Abubakar da Umar, Allah ya ƙara musu yarda, munanan abubuwa guda biyu: barin wajibi da aikata haram. Wannan da harshen Shari’a shi ake cewa fasiƙanci. Wata ƙila muna iya ƙarawa da wani abu na uku wanda ya fi biyun muni: saɓawa umarnin Annabi(SAW) da gangan, abinda yana iya zama kafirci, wanda kuma shi ƴan Shi’a suke nufi da wannan zargin tunda su a wajensu waɗannan Sahabban kafirai ne masu ridda. Wal iyazu billah!  
 Muna fata wannan zai zama gargaɗi ga masu karambani a cikin ilmin Musulunci da su sama wa kansu lafiya, su ƙyale masu ƙwarewa da fagensu.

•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 7: " ```Zuwan Shi’a Nijeria```" - na Prof. Umar Labɗo

 ✍ AnnasihaTv 

 Call/WhatsApp : 08063836963

 Twitter : https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)