DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [2]

DALILAN YAƊUWAR SHI’A A NIJERIYA [2] 




Akwai dalilai masu yawa da suka taimaka wajen yaɗuwar tafarkin Rafilanci a nan ƙasar.  Za mu duba muhimmai daga cikinsu. 

 Dalili Na Farko:  Gazawar Malamai 

Dalili na ɗaya kuma mafi muhimmanci, shi ne gazawar malamai a shugabancin jama’a da shiryar da su, da yi musu jagora da katangance su daga ɓata. Domin famintar wannan dalili za mu kasa malamai gida uku [kashi na farko ya gabata]

2. Kashi na biyu na malaman shi ne wanda za mu kira da sunan Ustazai. Wannan kashi ya haɗa da dukkan waɗanda suka yi karatun addini amma a zamanance, kamar waɗanda suka halarci makarantun Haya Muslim kuma suka yi karatun diflomomi ko digiri na fannin nazarin addinin Musulunci ko Shari’a a manyan makarantu da jami’o’in ƙasar nan. Kuma ya haɗa da waɗanda suka yi karatu a jami’o’in ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmi. Waɗan nan yawanci suna da kyakkyawar manhaja ta koyon karatu kuma ilminsu yana da faɗi da zurfi koda yake wasunsu, kamar waɗanda suka fita daga jami’o’in ƙasarnan, ilmin nasu faɗi gareshi kawai amma ba zurfi. Sai dai duk da haka suna samun kyakkyawan harsashi wanda yake ba da dama ga duk wanda yake so cikinsu da ya zurfafa. Suna tsakuro wani abu kusan daga ko wane fanni muhimmi na addinin Musulunci kamar Alƙur’ani da Hadisi (waɗan nan ba su da ƙarfi a manhajojin jami’o’in Nijeriya); Fiƙihu da Usulul Fiƙihi, Falsafa da Tauhidi (a makarantun Nijeriya yawanci Tauhidin Ash’ariya ake koyarwa); Tarihi da Sira; da kuma fannonin Luga dabam – daban irin su Adab, Nahawu, Sarfu, Balaga da ressanta uku, Aruli, da sauransu. Samun ƙaƙƙarfan harsashe na Luga yana zama tamkar wani mabuɗi ga Ustazai wanda suke buɗe taskokin ilmi da shi. 

 Kamar yadda Ustazai suka sha bamban a wajen ilminsu, da mai zurfin ilmi da mai cikin cokali, haka nan suka sha bamban wajen ayyukansu da halayensu da sadaukar da kansu ga addini. Akwai masu aƙidar Salaf, masu bin Sunna da yaƙar bidi’a, kamar yadda akwai ƴan gargajiya wajen aƙidarsu da fahimtarsu da rungumar bidi’a. Daga cikin waɗan nan na biyun akwai waɗanda suka fito daga gidajen malaman zaure, waɗanda suka fito daga gidajen sarautar gargajiya da masu karkata ga ɗariƙun Sufaye. A cikin Ustazai akwai masu yin wa’azi da waɗanda ba sa yi, da masu yaƙar bidi’a da ƴan ba-ruwanmu da waɗanda suka sadaukar da kawunansu domin koyar da mutane da aikin da’awa da waɗanda ba sa koyarwa sai dai a aji inda ake biyan albashi. 

 Yawanci waɗanda suka wayar da kan Musulmi dangane da tafarkin Rafilanci, suka bayyana ɓacinsa da sharrinsa da ɓatansa, suka yi fama don dakatar da yaɗuwar Shi’anci a tsakanin Musulmi daga cikin wannan kashi suke. Daga cikinsu akwai waɗanda suka yi amfani da koyarwa da wa’azi wajen yaƙar Shi’a kamar Shaihu Abubakar Mahmud Gumi, wasu sun yi amfani da huɗuba kamar Shaihu Abubakar Jibril Sakkwato, wasu sun yi amfani da alƙalumansu kamar Shaihu Aminuddini Abubakar Kano wanda ya fassara littafin Alkhuɗuɗul Arida na Muhibbud Dini Alkhaɗib zuwa harshen Hausa wanda a karon farko ya fallasa asirin Shi’a ga jamhurun Musulmi waɗanda ba sa karatun Larabci ko Turanci.

•••═══ ༻✿༺═══ •••
 - JERIN LITTAFAN SHI’A NA 7: " ```Zuwan Shi’a Nijeria```" - na Prof. Umar Labɗo

 *✍ AnnasihaTv* 

- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka;

 *Call/WhatsApp* : 08063836963


Post a Comment (0)