DEMOKURAƊIYYA

Demokuraɗiyya 



 1. 
Allah gwani Kai ne mafi hikima,
Ka ji ƙaina Ka yi mini rahama,
Domin ManzonKa mai alfarma,
Wannan da ya zo mana da ni'ima.

 2. 
Jama'a ga waƙar demokuraɗiyya, 
Tsarin nan na bayan mulkin soja, 
Wanda soji suka ba wa farar hula, 
Ragamar mulki a fage na siyasa. 

 3. 
An ce tsarin nan na jama'a ne, 
Kuma an yi shi don jama'ar ne, 
Domin kare haƙƙin jama'a ne, 
Dukiya da rayukan jama'ar dai. 

 4. 
Ka fito ka zaɓi wanda ka ke so, 
Domin ya yi maka abinda ka ke so, 
A sa'ili, sa'adda da inda ka ke so, 
Kuma cikin yanayi wanda ka ke so.

 5. 
Wannan shi ne batun da aka tsara, 
Amma sai ga shi ya zamo hira, 
Sai banƙare mu ake kamar fara, 
Manya da ƙanana muna ƙara. 

 6. 
Ko da ka zaɓi wanda ka ke so, 
A fage da tsari wanda ba ka so, 
Ƙarshe dai a ba wa wanda ba ka so,
Ya yi maka jagora wadda ba ka so. 

 7. 
Kenan demokuraɗiyya tai ƙarya, 
Aiyukan ga wasu ne kawai ke tafiya, 
Yayin da wasu ko ba a ko kallo, 
Ana ta buga su kawai kamar ƙwallo. 

 8. 
Ina kira ga 'yan demokuraɗiyya, 
Ku yi gyara da tsari na shiriya,
Ɓawon gyaɗar zalunci a ɓare, 
'Yanci da mutuncinta kar ya ɓare. 

#haimanraees 


Post a Comment (0)