CANJIN CANJI



Canjin Canji 

Da sunan Rabbana Allah,
Wannan wanda Ya yo canji.

Allahu, Al-Ƙaliƙu gwani,
Wannan da Ya yo kaji.

Allah don Alfarmar Sayyadi,
Ka tsare ni da sharrin ka ji.

Allah nunko dubun salatanKa,
A gare shi mai hasken ƙwanji.

Kasan ko babu awo ba haɗi,
A tsakanin gyaɗa da gurji.

Ga manzona, annabina,
Sayyadi mai yalwar ƙirji.

Kai na zaɓa, kai zan bi,
Ko ana niƙa ni da burji.

Canjin Canji nake kira,
Ku fito duk ku ji.

A da ana zagin su kura,
A yau kuma an hau su kaji.

Dawakai na haniniya,
Su zakuna kuma na gunji.

Wasu na kama ƙarafa,
Mu ko an bar mu da ledoji.

To tsaya ma kafinta,
Me ya kai shi karya gadoji.

Canjin iska ake so duniya,
Sai ake dasa sabon daji.

Maye dai ko ya kai fagen,
Su Ilu mai gani har hanji.

Na san ba ya iya mani,
Tun da Allah ya tsare ni.

Canjin shugaba muke so,
Mun manta canjin canji.

Canjin kawunanmu lallai,
Ku sani shi ne canji.

Canjin zuciyaramu,
Shi ne ƙaton canji.

Canjin halayenmu,
Shi ne asalin canji.

To kafin mu yi canji,
Sai mu canza kafin canji.

#haimanraees 

Post a Comment (0)