HASSADA
Mai hassada ya wahala,
Wanna ya faΙa juhala,
Ya yi wa kansa talala,
Da igiya yawan malala.
Da ma ka gane ka daina,
Kafin wataran ka ganka rana,
Ana yi ma ature da Ζuna,
Kai ko kana ta Ζara.
Yo in banda ba wa kai aiki,
Me zai kai ka neman ilimi ga jaki,
Ina fa za a gama makaho da tuΖi,
Balle a haΙa shi yin faΙa da zaki?
Magana ce dai nake ka duba,
Kafin ka fara nuna gaba,
Ka cire hassada a gaba,
Ka kama Manzona da Rabba.
In kuwa ka Ζiya to ka sani,
Kai tamkar mace ce ba zani,
Ka ga ko cikin 'yan zamani,
Ita ake gudu kamar zarni.
Allah mu dai ka tsare mu,
FaΙawa sharri a junanmu,
Hassada, gulma Ka tsare mu,
Daga mu har zuwa iyalanmu.
Allah mun tuba Ka shirye mu,
Kafin mutuwa Ka ganar da mu,
Laifinmu duka Ka yafe mu,
A aljanna Ka haΙa mu da Manzonmu.