NAZARI

NAZARI:


20 December 2020

A zaben da a ka yi a America tsakanin Trump da Biden, Zamu ga cewa daga cikin ƙasashen da su ka yi fatan Trump ya lashe wannan zaben sune :Saudiya, Masar, Turkiya da Russia. Hakanan waɗanda suka yi fatan Biden ya lashe wannan zabe akwai Qatar da China da ƙasashen tarayyar Turai(EU).

Abin la'akari a waɗannan kasashen zamu ga wasu ƙasashen da ba sa jituwa da junansu amma sun hade a bayan ɗan takara ɗaya, hakanan zamu ga wasu kasashen suna da kawance mai karifi da wasu amma sun rabu a goyan bayan wani ɗan takara.

Saudiya da Turkiya babu jituwa tsakaninsu hakan tsakanin Turkiya da Masar wanda ko ga maciji ba sa yi, Russia da Turkiya akwai jiƙaƙƙiya adawa tsakaninsu, hakanan tsakanin Saudiya da Russia babu wata jituwa tsakaninsu. 
Duk wannan sabanin na su amma sai gashi duk sun hade akan fatan Trump ya ci zabe.

Hakanan idan muka kalli ɗayan ɓangaren zamu ga Qatar ƙawar Turkiyace amma ta goyi bayan wani daban wanda Turkiya ba ta so, hakan China ƙawar Russia ce amma sun raba gari anan, ƙasashen(EU) ba sa jituwa da China, hakan itama China ba ta da wata alakar a zo a ga ni tsakaninta da Qatar, amma kuma duk sun haɗe a goyon bayan Biden.

Ba tare da ambaton dalilan waɗannan kasashen na goyan bayan wanda suke goyawa baya ba sabo da gudun tsawaitawa ba. 

Wannan shi yake nuna mana cewa siyasa ta ginu ne akan duba maslaha ba akan aɗifa da huce haushi ba, don kawai wanda kake adawa da shi yana goyon bayan wani kawai ka sabamai ka goyi bayan kishiyarsa don kawai ka bata mai, ko don wanda kuke da kyakkyawar alaka da shi ya goyi bayan wani kawai kaima ka rufe ido kace sai shi. A siyasa a na duba maslaha ne da cancanta ba soyayya da kuma huce haushi ko baƙantawa wani ba, har kaga wani lokacin ma inma ta kama har su shata layi su mai da ita kamar ƴaƙin Badar. Matuƙar al'ummarmu musamman ta Arewacin Nigeria ta fuskanci wannan karatun to za ta warware wani kaso mai girma daga cikin matsalolin da take fama da su

#Abm muhd Sani

Miftahul ilmi 
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://wa.me/message/C23PMZBORBTMH1
Post a Comment (0)