YADDA AKE BIYAN TSOHON BASHI !

YADDA AKE BIYAN TSOHON BASHI !



Tambaya
Salam. Ina da tambaya
Na ranci kudi fam biyu kamar shekaru (62) da suka wuce, ban biya ba.
In zan biya yanzu da haka fam biyun zan biya ko ko ya zaa yi ?

Amsa
Wa alaikum assalam
Wasu malaman sun tafi akan cewa zai biya kima ne, na kudin da ya ranta, misali Fam biyu me za ta iya siya a wancan lokacin, sai a bada kimarta a yanzu, saboda in an biya da adadinsu akwai cutarwa ga wanda ya ba da bashin, kuma yana daga cikin ka'idojin Sharia tunkude cuta gwargwadon iko.

Malaminmu Sheikh Ibnu Jibrin (Bajimin malami, mai amsa fatawa a Saudiyya) ya tafi akan cewa ana iya biyan kwatankwacinsu daga kudin da darajarsu ba ta faduwa kamar Dalar Amurka.

Allah Ne Mafi Sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
07- 03- 2023

Miftahul ilmi 
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://wa.me/message/C23PMZBORBTMH1
Post a Comment (0)