Istikhara

Istikhara 


1. Istikhara shi ne neman zaɓin da miƙa lamura zuwa gare shi kan duk wani ƙuduri da kake son cimma ko wasu lamura na rayuwarka (Bukhari, 6841).

2. A ƙa'ida, ana Istikhara ne kafin ka yi wa kanka zaɓi, ba (wai) har sai zuciyarka ta yi zurfi har ka kwallafawa ranka son abun ba. Ana iya yi kafin faruwar wani abu, kamar aure, canja muhalli da sauransu, domin neman zaɓin alheri.

3. Za ka yi alola, ka yi sallah raka'o'i 2 na nafila da niyyar Istikhara. Bayan ka idar sai ka ɗaga hannu ka karanta addu'ar Istikhara (ga ta nan a jikin hoton ƙasa). Kuma ko ba ka haddace ba, za ka iya karantawa daga littafi, ko maimaitawa daga 'audio'.

* Ba a yi sallar Nafila a lokutan da aka karhanta, mis. kafin fitowar rana (bayan sallar Asuba), lokaci da rana ta yi zawali da kuma bayan sallar La'asar (har sai rana ta faÉ—i).

* Za ka iya maimaita Istikhara sau ba adadi, har sai ka gamsu da zaɓin da ya bijiro gare ka, domin Ubangiji na son bayi masu naci, da neman kusanci gare shi (Muslim, 2664)

4. Ana son a yi Istikhara, da yaƙini, tare da fawwalawa Ubangiji lamari na duk sakamakon da ya biyo baya (shi ya sa ake son a yi kafin ka zurfafa a kan son abu) domin Istikhara tana da ƙarfin gaske, domin ka shigar da Ubangiji ne cikin lamuranka, shi kuma cikin hikimarsa zai ƙadarta abin da ya fi dacewa da kai, wanda ka fi buƙata, ba (wai) wanda ka fi so ba.

5. Idan a tsakanin abu 2 ne kake neman zaɓi (misali, mijin/matar aure), da sannu a hankali Ubangiji zai sa ma son ɗaya fiye da ɗaya, har ka ji ya fi kwanta ma a ranka, ka ji kafi samun nutsuwa da shi. Sai ka karkata gare shi, ka bar wa Allah sauran.

Idan kuma rabuwa ne, da sannu Ubangiji zai ƙaddaro wasu lamura da za su rage kaifi son abun a zuciyarka, har ka ji rabuwa da abin shi zai fi kawo ma kwanciyar hankali. Sai ka rabu da shi, ka fawwalawa Allah sauran lamari, ya maye ma da mafi alheri.

* Kar mu manta da ƙa'ida, ba sai ya ƙasance dama ka riga ka tsara son abun ba, ko ka riga ka tsara rabuwa da shi ba.

6. Ba gaskiya ba ne cewa ana ganin abun da ake neman zaɓi a cikin mafarki. Yawancin mafarki, malaman halayya sun ce, an fi yi kan abin da mutum ya fi kwallafa ransa a kai, ko yawan tunaninsa, ko ka kwanta da tunaninsa, mai kyau ne, ko maras kyau (Cynthia, 2017 & Harini, 2022).

7. Amfani yin Istikhara shi ne, zai sa ma tawakkali a zuciya, da samun nutsuwa kan duk abin da Allah ya ƙadartawa rayuwarka, ba tare da ka shiga damuwa ba, tunda ka bar zaɓin lamuranka a wajen Allah.

Duk wanda ya nemi zaɓin Allah a lamuran rayuwarsa, ba zai taɓa da-na-sani ba.

✍️Aliyu M. Ahmad 
16th Sha'aban, 1444AH
8th March, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Istikhara
Post a Comment (0)