MAFITA {06}
Duk da dai yawancin abubuwan da suke sanya Jinnul Aashiq ya shafi budurwa shi ne ma ke sanyawa ya shafi mai aure, amma akwai wasu abubuwan da matan aure ke sakaci da kiyaye su tayadda har shaidanu su samu damar yin nasara akansu, abubuwan su ne kamar haka:
1- Rashin tsafta, ko da kuwa kina al'ada ya kamata kirika tsaftace jikin ki, suturarki, dakinki da ma gidan ki baki daya.
2- Rashin kwanciya da tsarki ko alwala. Za kaga yawancin ma'aurata da zarar an gama saduwa ba sa iya yin tsarki ko wanka sai kaga sun kwanta barci abinsu cikin janaba, kuma irin hakan yana da matukar hatsari sosai, domin shaidanu suna samun damar cutar da mutum a irin yanayin.
Kamata yayi mutum a qalla idan har ba za ku iya yin wanka ba a daren (saboda wasu dalilai) to kuyi tsarki ku ta yadda za ku wanke wannan qazantar sannan sai kuyi alwala ko da sabi 1-1 ne, shi kenan alabasshi daga baya ko da asubah sai kuyi wankan janabar.
3- Kauracewa karatun Alqur'ani da sauraronSA. Rashin yin Azkaar a dukkanin bigiren da ake yinsa.
5- Kallace-Kallace marasa amfani da kuma yawan sauraron kade-kade da wake-wake a gida.
6- Qulla wata alaqa mai qarfin gaske da yin mu'amilar aure da wani namijin da ba mijinki ba. Allah ya kyauta.
7- Mace ta rika bayyana tsiraicinta ko wani bangare na jikinta a fili tana ganin ai acikin gida take, kuma irin haka akwai aljanun da suke ganin ki idan sun fitinu da ke sai kuga sun shafe ki.
8- Yin maganar batsa yana sanya shaidanun Aljanu da na mutane su aboci mutum.
Wadanan da ma wasu abubuwan da ban lissafo ba suna cikin abubuwan da suke yin sanadin shigar Jinnul Aashiq jikin matar aure. Allah ya kyauta.
Yanzu kuma za muji wasu daga cikin alamomin da matar aure ke gane tana tare da Jinnul Aashiq :
1- Za kaga mace mai aure tana yawan jin haushi ko ta rika yin fushi da mijinta a haka kurum ba tare da wani dalili ba.
2- Za kaga tana cikin fara'a da walwala a duk lokacin da mijin ba ya gida, amma yana shigowa sai duk tabi ta sauya, sai taji ranta yana baci taji ba ta son ma ganinshi.
3- Za suyi ta walwala da mijinta da rana, amma da zarar dare ya yi sai duk taji ta tsane shi kuma ba ta son ya kusance ta.
4- Taji tana yin mafarkin za tayi aure ga wani namijin dabam kuma a cikin baccin sai ta rika tambayar kanta tana cewa: Ta yaya zan auri wani alhalin ni kuma ina da wani auren?
5- A Lokacin da mijinta ke saduwa da ita sai ta rika jin kamar mace ce yar uwarta ba namiji ba, saboda ba ta jin komai.
6- Yawan jin ciwo a kasan cibiya wajan mahaifa ko ciwon mara da kuma ciwon baya a santar mahaifa.
7-Mafarkin ruwa, shanu, maciji, Kare da Mage/Missa/Kuliya/Kyanwa.
Insha ALLAH za muci gaba a rubutu nagaba.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)
Domin karin bayani:
👇👇👇
Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)
Gmail:
rismawy86@gmail.com
WhatsApp :
+2348031542026
Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine