MATSALAR ZUWAN AL-ADAH (Menstrual Disorder)

MATSALAR ZUWAN AL-ADAH (Menstrual Disorder)




Mafi akasarin matasuna famada matsalar zuwan al-adah wadda wasu yakansa sushiga damuwa,bisa rashin sanin yazasu maganceta,,matsalolin sune kamar haka.
1_ DYSMENORRHEA (pain menstruation).
matsalace dake haddasa al-adah mace take zuwa da zafi, wadda Shima yakkasu Kashi biyu:
a-spasmodic dysmenorrhea:
shikuma yafi ta'allaqada zafinsa wajen Mara (uterine) Kuma sai lokacin al-adah yakefaruwa, kusan Rabin mata sunafamadashi, yawancinsa yakan farawa daga shekara 17yrs zuwa 28yrs.
Kuma Yadanganta da wata takan finwata,Yadanganta da jin,dakuma motsa tsokarwajen,wani lokacin har rashin zuciya yakesawada gudawa.
b-congestive dysmenorrhea:
shikuma wannan yafi faruwa ga manya, yakansa ciwon baya,ciwon qugu,dakuma yawan baccin rai nababu dalili, Mafi akasari zafin yakan daukar kwana biyu zuwa uku kafin al-adah.
2_AMENORRHEA/OLIGOMENORRHEA,(Absence of menstruation).
shikuma wannan matsalace dake dauke zuwan al-adah gabadaya.
ababen dasuke kawoshi sunhad'ada, PID, qari a fibroids , endometriosis, matsalar kwayaar halitta(chromosomal defect)Kamar tuner syndrome, asalina ahali,sadai sauransu
3_MENORRHEA (Yawaitar fitar jinin al-adah).
wannan shikuma yakan faru kodai yayi tsawo,kokuma yakezubada yawa, yakan haddasa qari a ovaries, da PID, dakuma grandier cell tumour, hormonal imbalance. up
4_EPIMENORRHEA (daurin juyowar al-adah),
Mafi akasarin mata sukanyi cycle dinsu awajen 26-28day, shikuma wannan yakan juyowa daga 14-21day, wannan yakan farune Mafi akasarin idan anyi abortion (zubarda ciki),kokuma haihuwa.
5_METRORHAGIA:
shikuma wannan matsalar tanasa zubar jini(bleeding) haka kawai karazube, Kakasa ganewa na al-adane ko akasin haka ,
yawanci wannan yakanfarune saboda cututtuka Kamar, trachomonas, vaginatitis, cervical erosion,incomplete abortion,PID dasauransu..........

MATAR DA TA SABA AL'ADA KWANA 3, 4, KO 5 YA DAUKE AMMA YAI KWANA DAYA KO BIYU YA DAUKE ME HAKAN KE NUFI ❓❓

Wannan shi ake Kira Shorter Bleeding Wanda mafi yawa alamun ciki kesa a samu Wannan.

Duk Matar da taga Haka matakin farko shine ayi Awon ciki a tabbatar.

Kada wannan yasa a damu, a dukufa neman maganin zuwan al'ada daga karshe a zubar da cikin da aka Dade ana nema ga wasu Matan.

Fara al'ada ta kwana Daya ko biyu ta tsaya Rana Rana Babu zato Babu tsammani Yana Daya daga cikin alamomin shigar Ciki, wannan Yana faruwa mafi yawa midway tsakanin ovulation da Kuma lokacin da mace take tinanin zuwan al'adar ta, tana ganin jini sau Daya ko biyu saita nemesa ta Rasa.

Wanann shine alamar implantation bleeding.

Yana faruwa lokacin da mace tayi Shirin ganin al'adar ta, ko take tsammanin zuwan al'adar ta.

Wallahu AAlam....👏
Post a Comment (0)