HANI GA MUMMUNA

HANI GA MUMMUNA 




Wata rana wani Malami daga cikin magabata ya aiki dansa kasuwa ya siyo hanta, da yaron ya dawo sai ya dakko wuka mai kaifi ya yanyanka hantar nan,.. tafiyarsa ke da wuya sai magen gidansu to zo tana lasar wannan wukar saboda karnin jinin dake jikin wukar, a daidai lokacin da take lasar wukar ba ta san cewa harshenta take yankawa ba. Da yaron ya fahimci cewa lasar kaifin wukar da take yi [duk da ita dadi take ji, amma harshenta take yankewa] sai ya koreta. Sai ta dinga gurnani tana nuna ba ta ji dadi da ya hana ta abin da take yi ba. Sai yaron ya ce: [a bayyane] "Kina cutar da kanki don na hana ki, shi ne kike jin haushi na?" Sai Malamin nan ya jiyo shi yana magana. Sai ya ce: "kai kuma da wa kake magana kai kadai?" Sai ya ce: Baba [Malam] magenmu ce take lasar wukar da na yanka hantar da na siyo, tana lasa; tana yanka harshenta, shi ne na kore ta, shi ne take min gurnani; tana jin haushi na. Sai Malamin ya ce: "To ai ba mage ba ma, mutane ma idan suna aikata abin da zai cutar da su [munkari] idan ka hana su, ko ka yi musu magana, sai su ji haushinka. Sai yaron ya ce: To ai kuwa kawai sai a kyale su, tunda cutarwa su ta shafa. Sai malamin ya ce: A'a, idan ka ga ana aikata munkari lalle ka hana, idan sun hanu, kun tsira baki daya, idan kuma ba su hanu ba, to kai ka tsira, su kuma azaba na iya riskar su idan ba su tuba ba. Idan kuwa ga gani ka yi shiru, to azabar idan ta zo na iya hadawa da kai.

Darasi:
1. Hana munkari yana sa masu aikata laifin su ji haushinka
2. Ba a daina hana munkari don wanda za a hana zai ji haushi
3. Hana munkari kubutar da kai ne
4. Rashin hana munkari na jawo barna gamammiya mai yawa ga al'umma.
5. Aikata munkari yana da dadi ga mai aikatawa.
 6. 

Allah ya ganar da mu. Allah ya tabbatar da mu a kan daidai, amin

~~ Sheikh Aminu Bala
Post a Comment (0)