KUNDIN MA'AURATA // 18

KUNDIN MA'AURATA // 18





WACE MACE CE TA QWARAI?
Galibin masu neman aure a yau za ka taras rana guda tal suka qyalla ido suka hanko wace suke kwadayin aurenta, in ko haka ne akwai abubuwa da dama wadanda ka yi kuskuren dubawa, zai yuwu wace kake da buqatar aure ba ita ce wace kake ganin ta dace ba, don ta qwarai ba ta da arhar da za a iya gano ta da kallo guda, iya wanka da karairaya da dadin baki ba su ne ma'aunin da ake gano mace ta qwarai ba, akan gano ta ne ta hanyoyi da dama, ciki da tsoron Allah kamar yadda muka karanta a baya, da haka ne za ta zama mai bauta, ta kare kanta da mijinta, ta kiyaye mutuncinsa da sirrorinsa.
.
Mace ta qwarai ba za ta ba da damar da za a kalli maigidanta ko a kalle ta a raina girmansa, arziqinsa da mutuncinsa ba, za ta yi iya qoqarinta wajen kare mutuncinsa da dukiyarsa da zumuncinsa, za ta kyautata mu'amallarta da 'yan uwan mijinta da surukanta wato uwayen mijinta, takan kiyaye irin mu'amallar da za ta yi da abokansa, a kowani lokaci takan dauki gidanta a matsayin wata masarauta da take jagoranci a matsayin sarauniya, da haka ne za ta kula da duk wadanda suke qarqashinta da adalci.
.
Koda yake mun sani cewa namiji shi ne maigida a shar'ance, amma zahiri ya nuna cewa bai da lokacin zama a cikinsa, galibin maza in suka bar gida da sanyin safiya sai kuma maraice yayin da suke dawowa a jigace, mafi yawansu ba sa iya kiyaye abin da suke son sani sai wanda aka gaya musu, in mace ta kirki ce takan toshe duk wata baraka a lokacin da maigidanta bayanan, in ya dawo kuma takan gaya masa barakar da yadda ta bi wajen toshe ta, in ma ba ta tosu ba takan gaya masa don ya san yadda zai yi da ita, shi ya sa gida kan gyaru a dalilinta ko ya baci saboda yanayin yadda take.
.
Idan aka sami mace ta qwarai takan zama tamkar madubi ne da ake ganin surar maigidan, komai za a yi wanda ya shafi maigidan in aka ganta shi kenan, ko kafuran da, in suka tashi kashe wani qasurgumi ba sa barin iyalinsa saboda tsoron abin da zai biyo baya, ita ce take iya qoqarinta wajen sanya 'ya'yanta su biyo ubansu dari bisa dari, masamman idan ya kasance uban nasu na gari ne, da wannan babban aiki za mu gano cewa hanyar zaqulo irin wannan macen bai da alaqa da kalar fatan mace ko kyawun qirarta, kamar yadda ya yi nesa da wayewarta ta zamani ko abin hannunta ko na mahaifanta.
.
Dabi'u ne wasu gadonsu ake yi, wasu koyo ake yi a makaranta kamar tsoron Allah da ibada, wasu kuma a gida ake dauka kamar ladabi da biyayya, kau da kai ga dukiyar maigida, tsafta da tsaftacewa, kwalliya da iya girki, sai kuma tausayi da sanin qimar namiji, in kuwa haka ne to sanin gidan da yarinya ta taso ya fi sanin makarantar da take karatu, abin takaici kala ya fi mana komai, shi ya sa 'yan matan ba su damu da nuna mana tarbiyyarsu ta gida da makaranta ba kamar yadda suke kashe kudinsu a yau wajen gyaran fatar fuska da hannu da qafa, inda za mu iya kallo, wannan ya fi biya musu buqata.
.
Da yake mu a matattararmu mace ba ta ganin namiji ta ce "Wannan ya yi min" ta fara shirye-shiryen nemansa dole dai sai wanda ya zo mata, duk da haka tana da damar da za ta nuna kwadayinta ga wanda ta yaba wa addininsa da dabi'unsa, ba za ta furta ba amma hanyoyin da 'yammata suke da su na isar da saqo ga namiji suna da yawa, wata rana na fito Rogo zan je Maqarfi, a daidai Filatan wata yarinya fara ta hau motar, ba a jima ba na ga ta fara kulawa da wani saurayi kusa da ni, don lokacin da aka tambaye shi kudin mota bai da canji, sai nan take ta biya, da zammar in muka isa can zai nema ya ba ta, tana tare da mahaifiyarta amma ba ta damu ba, sai jansa da magana take yi.
.
Bayan mun sauka na yi gaba na bar su ban san yadda suka qare ba, amma da na dawo tasha zan hau motar Kura na ji abokinsa yana zarginsa da rashin karbar tayin da aka yi masa, shi kuma yana kare kansa da cewa mahaifiyar yarinyar tana wurin, ban san dai yadda suka qare ba, amma yawan gaisuwa da fara'a da tambayar abokan mutum ina yake, da dan yi masa qananan hidindumu wadanda 'yanmata suke kira mutunci a yau, duk za su iya shigar da saqo har inda ake so, ni na ga budurwar da ta matsa sai wani yaro ya riqa koyar da ita, abin mamaki uwayen yaron ne da kansu suka roqe shi da cewa za ta riqa zuwa dakin mamansa yana koyar da ita, hujjarsu da haka wai sun ga tana da qoqari kuma ba ta da ginshiqi shi ya sa suka ga ya dace su taimaka mata.
.
Sai bayan ta aure shi muka sami labarin ashe ta ishe su ne da maganarsa suka taimaka mata, a birnance kuwa ga hanyoyinan sama da qirgar yatsu wadanda mace take da su wajen nuna buqatunta ga wanda take so ba sai ta wahalar da bakinta ba, abin da take buqata kawai ta harbi zuciyarsa ta qyale shi, da kansa zai kawo kansa, a irin wannan yanayi magana ba tata ba ce, amma kuskuren da mace za ta yi shi ne ta yi zaton cewa mu'amallarta da namiji a lokacin nemanta ita ce hanyar da za ta gano cewa shi na qwarai ne ya dace ta yarda da shi ko a'a, ita ma tana buqatar lokaci, ta sa 'yan uwanta maza su binciko mata, sirrin namiji sai namiji irinsa, in kina shakka ga maigidankinan, kullum sabbin abubuwa kike gani.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)