KUNDIN MA'AURATA // 17
DON ME KAKE BOYEWA?
Ba ina adawa da zuwan saurayi gidan budurwa hira ba ne, don na yi kuma ba zan ce ya zama halas ba, amma wace uwar ake tsinanawa matuqar ba a fitowa a nuna wa juna gaskiya? In kana da wata dabi'a fito ka nuna mata, kar ka ji tsoron cewa za ta iya rabuwa da kai, wani yana da saurin fushi, matsanancin kishi, fada ta ba gaira ba dalili, mugun son shimfida a kowani lokaci, da dai wasu abubuwa da kake ganin ba za ku daidaita a kai ba, ka nuna mata, in ta yarda shi kenan, wannan ya fi sauqi sama da a ce ka boye in ta shugo gidanka ku fara yaqin basasan da bai da iyaka, na taba ji wata tana gaya wa saurayinta cewa "Ni duk fadan da za ka yi ba zai dame ni ba, amma kada ka yi min a gaban jama'a" alal aqalla za su fahimci juna anan, kowa ya san abin da abokin zamansa ba ya so da wanda yake so.
.
Zan so ku daidaita a kan wasu abubuwa, mu dai mun taba aurar da wata yarinya sai maigidanta ya ce bai son kayan daki, ya tsaya a kan ta sayar da su ta sayo kujeru, qarshe hakan aka yi, kenan ya dace a san abubuwan da ba a buqata ta zo da su tun da wuri, babu laifi in ka san cewa za ta iya cin irin abincin da za ka riqa ba ta, ba sai an yi ittifaqi a kai ba, amma in ka san iyalinka ba za ta yi aikin gwamnati ba, ko ba za ta ci gaba da karatun boko ba, to ka daure ka fada mata gaskiya tun kafin a kai ga an daura auren.
.
Na san mutane guda biyu, dayan matansa 3, suka nemi su ci gaba da karatu, ya ce bai da matsala zai iya daukar nauyinsu, amma ba zai yarda da aikin gwamnati ba, da suka ji haka sai suka fasa, wadannan ma bayan aure ne, amma akwai wata da suka yi alkawarin cewa zai bar ta ta ci gaba da karatu bayan aure, abin takaici sai ya ce sam bai san wannan maganar ba, tana tare da shi, amma duk lokacin da ta ga sa'o'inta sun dawo makaranta ko wurin aiki sai ta ce maigidanta ya cuce ta, kuma ba ta damuwa a gaban kowa takan fada.
.
Wasu hatta maganar fita unguwa ba ya yarda da shi, yana ganin wannan shi ake kira kulle, na ga mutumin da matansa suke fita unguwa da asuba su dawo da daddare, duk dai saboda tsaro, na ce yana da gaskiya amma zai yi kyau ya gaya wa wanda zai aura dabi'unsa, don kar a zo ana ja-ni-in-ja-ka bayan aure, akwai wadanda samsam ma ba su yarda da maganar zuwa unguwa ba, ko uwayen yarinya ba sa ganinta in ba salla ko wani abu mai girma ba, to mutum in ya san don Allah yake abu bai dace ya boye komai ba, lallai musulmai su tsaya a kan sharuddansu, in har ka fadi yadda kake da wahala ka ji ana zagi ko zargi bayan aure.
.
Yadda za ka san bata wa juna lokaci ake yi a wuraren zance akan daura aure ma'auratan kullum sukan zauna daga qarfe 9pm-11pm na tsawon shekara 1-4 amma ba su san dabi'un juna ba, saboda ba abin da suke yi kenan ba, qoqarin kawar da sha'awa kawai ake yi ta wurin mannuwa da juna, tsotson minti da wasa da hannu, irin wannan ne bayan aure sai macen ta ga kamar wani namiji ta aura ba wanda ta sani ba, duk halin da ta san su da shi ya canja, a gaskiya dama ba sanayyar aka yi ba, wani abokin aikina ya gaya min cewa kusan shekararsa 3 yana neman aure amma ya zauna ta matar sau 3 ne kacal.
.
Da na gwada sai na ga to ni me nake ce mata? Duk da cewa ni shekara 4 na yi ina nema, kuma na je gidansu ya kai sau 6, nakan je bayan magriba, duk da dan bata lokacin da ake yi wurin shirye-shirye in na ga issha ta gabato nakan gudu, kenan nakan sami kamar minti 20 zuwa ishirin da wani abu, in na kwatanta da abokina to na matsa qwarai, sai dai kuma in na ga wasu to nawa ya dan fi kyau, don su ba a cikin gidan ba ne, a waje suke zama, su biyu kacal da daddare a saqo sannan a cikin duhu kamar marasa gaskiya, ban san wace fahimta ce da ba a yinta a cikin haske sai a duhu ba, kuma kullum sai an yi ta kamar masu haddar Qur'ani.
.
Irin wannan zaman na bata wa juna lokaci shi ne ake kira da zaman soyayya wanda mace in ba ta yi shi ba take ganin kamar an yi mata auren dole, a haqiqanin gaskiya ba haka lamarin yake ba, soyayya ba a yin sa kafin aure, akan ba da damar a yi wannan zaman ne don a fahimci juna, kowa ya san hali da dabi'un wanda zai aura, ko dai su sami qarfin gwiwar ci gaba, ko su sami matsayar hanqure wa juna, su san abubuwan da kowa yake so da wadanda ba ya so, don su kiyaye abin da za su aikata da wadanda za su guda.
.
Soyayya ba ta amsa sunanta sai ta cika, a kowani harshe ne kuwa, a turance kalmar "love" sam ba ta tsaya kan abin da kake ji a zuciyarka na qaunar wani ba, ta shafi ma duk abin da za ka yi da gabobinka a dominsa, haka "Hub" a Larabce, a Hausa ma tana da fadi sosai dole marubuta su rarrabewa jama'a bambancin dake akwai a tsakanin dan kuka da dan tsamiya, soyayya ta gaskiya takan fara daga ranar da mace ta sa qafa a dakinka, muguwar sha'awa kuma takan qare daga watan da ka fara sanin iyalinka sai sha'awar dabi'a ta ragu, wadanda suka san ma'anar soyayya sukan tsufa da ita, kuma ana ganinta tare da su, wadanda suka yi mata gurguwar fahimta sukan ce ta qare daga shiga dakin aure.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248